’Yan bindiga sun ƙaƙaba wa ƙauyuka harajin N10m a Neja

[ad_1]



’Yan bindigar da ke addabar yankunan karkara sun kaƙaba sun ƙaƙaba musu haraji da ke kaiwa Naira miliyan 10 a Ƙaramar Hukumar Mashegu Jihar Neja.

Rahotanni sun nuna cewa an umarci al’ummomin yankunan Babban Rami da Kaboji su su biya Naira miliyan biyu-biyu.

Yankin Sabon Rijiya da Sabon Rami an umarce su da su Naira dubu 500, yayin da aka umarci ƙauyukan da ke kusa da Dajin Keji su tara Naira miliyan 10 gaba ɗaya.

Haka nan, ana ƙaƙaba wa al’ummar Khizi an kaƙaba musu harajin Naira miliyan shida, da wa’adin ranar Juma’a, 3 ga Oktoba, 2025.

Wani mazaunin yankin ya shaida wa Aminiya cewa: “’Yan bindigar sun kashe mutane da dama kuma suna ci gaba da kai hare-hare. Sun kaƙaba haraji ga ƙauyukan da ke gefen dazukan Ibbi da gandun dabbobi na Kanji National Park.

“Muna roƙon gwamnati ta gaggauta ɗaukar mataki, saboda yawancinmu manoma ne, kuma sama da kashi 90 cikin 100 na amfanin gona bai ma kai girbi ba.”

Wata majiyar ta bayyana cewa da dama daga cikin manoma an kashe su ko an yi garkuwa da su a gonakinsu, yayin da matafiya ke fuskantar kwanton ɓauna a kan tituna, wasu kauyuka kuma ana kona su gaba ɗaya.

Rundunar ’yan sanda a Jihar Neja ba ta fitar da wata sanarwa kan lamarin ba zuwa lokacin haɗa wannan rahoto.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *