ICPC ta tsare tsohon shugaban NIMASA, Bashir Jamoh




Jami’an Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa ta ICPC sun tsare tsohon shugaban Hukumar Kula da Harkokin Ruwa da Tsaro ta Najeriya (NIMASA), Bashir Jamoh.

Majiyoyi masu inganci sun shaida wa Aminiya cewa Bashir, wanda ya jagoranci hukumar daga 2020 zuwa 2023, har yanzu yana tsare a hannun hukumar a lokacin da ake rubuta wannan rahoto.

Ɗaya daga cikin majiyoyin ya ce an kama tsohon shugaban na NIMASA ne bayan ya gaza amsa gayyatar da hukumar ta yi masa sau da dama, bayan korafe-korafe da aka shigar a kansa.

A cewar majiyar, ɗaya daga cikin korafe-korafen ya zarge shi da amfani da hanyoyin saye da sayarwa na bogi domin amfanar da kansa, abin da aka bayyana a matsayin amfani da mukami ta hanyar da ba ta dace ba.

“ICPC ta kama shi bayan ya gaza amsa gayyatar da aka yi masa a lokuta da dama. Ana bincikensa kan amfani da mukami ba bisa ka’ida ba a lokacin da yake jagorantar NIMASA,” in ji majiyar.

Da aka tuntubi mai magana da yawun hukumar, John Odey, ya tabbatar da kama Bashir amma ya ƙi bayyana cikakkun bayanai kan zarge-zargen da ake masa.

“Ina jiran samun cikakken bayani kan dalilin kama shi, zan maka karin bayani daga bisani,” in ji mai magana da yawun na ICPC.

Menene NIMASA ke yi?

Aminiya ta ruwaito cewa NIMASA hukuma ce ta gwamnati da ke da alhakin tsarewa da kuma inganta harkokin ruwa a Najeriya.

takamaimai, hukumar na mayar da hankali kan tsaro, kariya da ci gaban harkar ruwa.

Ayyukan NIMASA sun haɗa da tabbatar da tsaro da kariya ga jiragen ruwa, inganta ci gaban harkokin ruwa, kare muhallin teku da kuma tabbatar da bin dokokin ruwa da ƙa’idoji.

Binciken zargin almundahanar Naira tiriliyan 1.5

A shekarar 2021, Jamoh da kansa ya rubuta wa Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa (EFCC) domin ta binciki zargin almundahanar Naira tiriliyan 1.5 da aka yi masa.

Lamarin ya biyo bayan zargin da wani mai suna Jackson Ude ya yi masa, inda ya ce Jamoh ya karkatar da Naira tiriliyan 1.5 zuwa asusun ajiyarsa, tare da zargin cewa ya karkatar da dala miliyan 9.5 zuwa wani asusu daban da aka gano yana da alaƙa da shi.

A cikin jerin sakonni a shafin Twitter, Ude ya rubuta: “Bashir Jamoh, DG na NIMASA, ya shaida wa abokansa cewa bai san komai game da Naira tiriliyan 1.5 a kowanne asusu ba. Ya ce labarin ƙarya ne. Zan fitar da hujja daga baya.”

A cikin wasikar da ya aika wa EFCC, Jamoh ya nemi hukumar ta gudanar da cikakke kuma zuzzurfan bincike kan zarge-zargen.

Ya ce binciken zai bayyana gaskiya kuma ya fayyace lamarin a idon jama’a.

Sai dai bincike ya nuna cewa EFCC ba ta dauki wani mataki na zahiri kan lamarin ba.




Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *