Za a iya kama ni a kowane lokaci — El-Rufai
Tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai, ya ce Gwamnatin Tarayya ƙarƙashin jam’iyyar APC na iya kama shi a kowane lokaci.
El-Rufai, wanda yanzu jigo ne a jam’iyyar adawa ta ADC, ya ce ana matsa wa ’yan siyasa su koma jam’iyya mai mulki ko su ci gaba da zama a cikinta.
Ya bayyana hakan ne yayin wata hira da ya yi da BBC Hausa a ranar Laraba.
Ko da yake ba a kama shi ba kawo yanzu, El-Rufai ya ce an riga an kama wasu daga cikin makusantansa.
A baya-bayan nan, ya tsananta sukar Gwamnatin Shugaba Bola Tinubu da kuma jam’iyyar APC, wadda ya yi gwamna a ƙarƙashinta na tsawon shekara takwas.
“Mutum huɗu da muka yi aiki tare da su a Kaduna an kama su; don haka lokaci ne kawai ya rage kafin su zo su ni ma su kama ni,” in ji El-Rufai.
Wannan furuci nasa na zuwa ne a daidai lokacin da aka kama tsohon Ministan Shari’a kuma Babban Lauyan Gwamnatin Tarayya, Abubakar Malami, wanda a yanzu haka ake tuhumarsa.
Hukumar Yaƙi da Masu Yi wa Tattalin Arziƙi Zagon Ƙasa (EFCC), ta tuhumi Malami da laifukan almundahana.
Daga bisani, hukumomi sun sake kama shi, bisa zarginsa da hannu wajen ɗaukar nauyin ta’addanci.
Malami, wanda ɗaya ne daga cikin manyan ’yan adawar Shugaba Tinubu, ya musanta dukkanin zarge-zargen da ake masa.
Ya bayyana su a matsayin shafa baƙin fenti biyo bayan ficewarsa daga APC zuwa ADC.