Jirgin ƙasa ya murƙushe babur mai ƙafa uku a Jos




Wani jirgin ƙasa ya murƙushe babur mai ƙafa uku a shataletalen Abbatuwar Phototake da ke birnin Jos a Jihar Filato.

Aminiya ta ruwaito cewa an tabbatar da mutuwar direban da wani fasinja guda ɗaya, tare da jikkatar wasu mata biyu.

Shaidun gani da ido sun ce hatsarin ya faru ne da misalin ƙarfe 10:00 na safiyar ranar Laraba, bayan tasowar jirgin daga Bukuru zuwa Jos.

Wasu mazaunan yankin sun ɗora alhakin faruwar hatsarin kan rashin mutumin da ke kula da shingen tsallaka titin jirgin, wanda ya ratsa titin motoci a daidai shataletalen Abbatuwar Phototake.

Sai dai mai magana da yawun tashar jirgin ƙasa ta Jos, Adam Abdullahi, ya musanta zargin, yana mai cewa direban babur ɗin ne ya ƙi tsayawa duk da gargaɗin jami’in da ke wurin, wanda hakan ya jawo jirgin ya yi ciki da shi.

Bayanai sun ce wannan lamari dai ya fusata mazauna yankin, inda suka shiga jifan jirgin da duwatsu, wanda hakan ya sa jirgin ya gaggauta ƙarawa gaba domin kauce wa tashin hankali.




Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *