Ƙungiyoyin Ɗariƙun Sufaye Sun Maka Gwamnan Kano A Kotu
[ad_1]
Kungiyoyin Darikun sufaye da dama sun maka gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, tare da Kwamishinan ‘Yansanda na jihar da Babban Lauya kuma Kwamishinan Shari’a, kan yadda suka ki gudanar da hakkin da ya rataya a kansu kan batanci da ake zargin malamin Musulunci, Malam Abubakar Lawan Triumph ya yi wa Annabi Muhammad SAW.
An bayyana karar ne a cikin wata takarda da ke yawo a kafafen sada zumunta, mai taken “Dambarwar Shari’a a cikin batun Malam Abubakar Lawal (Lawan Triumph) a Babbar Kotun Shari’a ta Jihar Kano.”
A cewar takardar, wadanda ake kara da suka hada da Gwamna Yusuf, Kwamishinan ‘Yansanda, da Babban Lauyan gwamnati, an zarge su da gazawa wajen aiwatar da ayyukansu na doka na gurfanar da masu aikata manyan laifuka a karkashin Dokar Shari’a ta Jihar Kano ta 2000 da Dokar Laifukan Intanet ta 2024 (kamar yadda aka gyara).
Kungiyoyin da suka yi hadin gwiwar shigar da karar sun hada da Interfaith Partners for Peace and Development, Fityanul Islam of Nigeria, Sairul Qalbi Foundation, Tijjaniyya Youth Enlightenment Initiative, Hablullahi Mateen Foundation, Dariqa Qadiriyya of Nigeria, Kadiriyya Youth Awareness, Kadiriyya Riyadul Janna Kofar Na’isa, Ashabul Kahfi Foundation, da Majmau Ashabul Yameen.
LEADERSHIP ta ruwaito cewa, takaddamar da ta shafi Malam Lawan Triumph ta fara ne a watan Satumba bayan da wasu ƙungiyoyin addini suka ɗauki wasu wa’azozinsa a matsayin ɓatanci ga Annabi SAW, wanda ya haifar da cece-kuce da muhawara a faɗin jihar. Wannan lamari ya sa gwamnatin jihar ta shiga tsakani ta hannun Majalisar Shura ta Jiha, wadda aka ba da umarnin gudanar da bincike kan zarge-zargen.
Bisa umarnin gwamnati, Majalisar Shura bayan ta tantance wa’azozin malamin, sannan daga baya ta gayyace shi don zaman tattaunawa.
Tun bayan zaman, har zuwa yanzu babu wata sanarwa a hukumance daga gwamnati kan sakamakon zaman da kwamitin Shura ya yi akan Malam Triumph.
Har zuwa lokacin rubuta wannan rahoton, gwamnatin Jihar Kano ko rundunar ‘yansanda ba su bayar da wani martani a hukumance kan karar ba.
[ad_2]
Source link