Majalisar Dattawa ta dakatar da tantance sabon Ministan Tinubu
[ad_1]
Majalisar Dattawa ta dakatar da aikin tantance Dokta Kingsley Tochukwu Udeh, SAN, wanda Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya naɗa domin zama minista, sakamakon rashin gabatar mata da rahoton jami’an tsaro a kansa.
Shugaban Majalisar Dattawan, Godswill Akpabio, ne ya bayyana haka yayin zaman majalisar na ranar Laraba, inda ya ce ba za su ci gaba da tantancewar ba sai an samu cikakken rahoto daga hukumomin tsaro.
A ranar Talata ce Shugaba Bola Tinubu ya aike wa majalisar sunan Mista Udeh, ɗan asalin Jihar Enugu cikin wata wasiƙar neman sahalewarta.
“Ina farin cikin miƙa sunan Dokta Kingsley Tochukwu Ude, SAN, domin tabbatar da shi a matsayin minista. Ina fatan majalisar za ta yi la’akari da wannan buƙata cikin gaggawa kamar yadda aka saba,” in ji wasiƙar shugaban ƙasan.
Tinubu ya naɗa Udeh ne bayan murabus ɗin da Ministan Kimiyya, Uche Nnaji ya yi, bayan zargin da aka yi masa na gabatar da takardar shaidar kammala karatu ta bogi, wanda kuma shi ne minista ɗaya kacal daga Jihar ta Enugu
Mista Udeh wanda yanzu haka shi ne Antoni-Janar kuma Kwamishinan Shari’a na Jihar Enugu, ya shahara da ƙwarewa a fannin doka da kare haƙƙin ɗan Adam.
Ana iya tuna cewa, a watan Oktoban da ya gabata ne Tinubu ya naɗa Dokta Bernard Mohammed Doro daga Jihar Filato a matsayin sabon minista a gwamnatinsa.
Naɗin Dokta Doro na zuwa ne bayan zaben Farfesa Nentawe Goshwe Yilwatda da aka yi a matsayin Shugaban jam’iyyar APC na ƙasa a watan Yuli, wanda a baya yake riƙe da muƙamin Ministan Harkokin Jin Kai da Rage Talauci.
Mai dangantaka
[ad_2]
Source link