Garkuwa: TETFund, NSCDC Sun Hada Gwiwa Don Magance Tsaro A Makarantu

[ad_1]

Gidauniyar manyan makarantu tare  (TETFund) tare da hukumar farin kaya ta  (NSCDC) sun yi hadin gwiwa domin su kara bunkasa lamarin tsaro a wuraren kwana na manyan makarantun Bijeriya domin ayi maganin yawan  hare- haren  da ake  kaiwa manyan makarantu.

Shugaba kuma babban kwamanda na NSCDC, Farfesa. Ahmed Abubakar Audi ,wanda ya jagoranci tawagar manyan jami’an hukumar lokacin da suka kai ziyarar ban girma zuwa hedikwatar ma gidauniyar manyan makarantu da ke  Abuja,  yace duk da yake dai an samu raguwar kai hare- hare zuwa manyan makarantun Nijeriya, hukumar ta bukaci gudunmawar rundunar  da kuma masu ruwa da tsaki domin, a samu da,a ta maganin su ‘yan ta’addar.

  • Kasar Sin Na Da Kayayyakin Tarihi Na Halittu Na Duniya Guda 15
  • Ma’aikatar Harkokin Wajen Sin Ta Yi Liyafar Sabuwar Shekara Ta 2026

Babban Sakataren gidauniyar TETFund, Arc. Sonny Echono, tare da manyan jami’an gidauniyar.

Tattaunawar da suka yi  ta maida hankali ne kan wajen hadin gwiwa domin a kafa kungiyar tsaro mai zamn kanta a wuraren kwana na makarantun Nijeriya,ga kuma bada taimako na horad da wadanda za’a dauka ’da wurin da za ayi horarwar bincike,da kuma yadda duk inda ake karatu ya zama bai da matsalar rashin tsarom ga kuma yadda za a kara bunkasa wurin neman karatu da tsaro.

A na shi jawabin, Audi ya bayyana irin gudunmawar da jami’an farin kaya na NSCDC suke badawa ga lamarin tsaro na Nijeriya, a matsayin yadda hukumar ta kasance ta daya  wajen kare abubuwa masu amfani da suka hada da abubuwan more rayuwa, da kaddarori, da kuma makarantu.

Ya nemi gudunmawar hukumar ta TETFund da cewar ta taimaka wajen daga girman wuraren horarwa  shida na NCSDC, musamman  kwalejin lamurran da suka shafi tsaro da ke Abeokuta, domin tabbatar da ana samun ci gaba na Kwalejin saboda taimakawa Jami’ai wadanda suke da  sha’awar ci gaba.

Ya ce mganar gaskiyar rundunar tana aikinta na kare makarantu a kowne sako da lungu na Nijeriya.

Ya ce; “dan kana bibiyar lamarin yanzu, da yadda abin yake , za ka gane cewa yanzu yadda ake kai hare- hare ya canza ba kamar yadda abin yake ba a shekarun baya.

“Idan baka da tarihi ba, an fi yawan kai hare- hare tsakani shekarun 2001, 2002, da kuma 2003. Sai bayan abin auku ne sai Nijeriya ta kaddamar da tsarin samar da tsaro a makarantu, bayan ziyarar Gordon Brown, da kuma yadda aka fada daukar nauyin tafita da lamarin.

“Abin fara ne, lokacin da akai kai ma ‘yan makarantar mata ta Chibok daga nan kuma sai abin ya cigaba da faruwa. Bada dadewa bane kuma sai kai hare- haren ya tsya, duk kuwa da yeka akwai wadansu wuraren da akan samu lai hare- haren, sai dai kuma an samu shawa kan lamarin.

“Maganar gaskiya,rundunar  ta NSCDC duk wani lamarin da ya shafi samar da kulawar kawo tsaro na makarantu tamkar ma ya shafi dukkan al’umma ne, wurin da duk masu fada ajin suna nan, hukumomin tsaro, tare da masu fada aji da suka hada da gidauniyar manyan makarantu (TETFund) Hukumar kula da al’amuran jami’oi (NUC) dukkannin  makarantun,su kasance sun hada kansu,domin aiki tare.

“Shi yasa jami’am ‘yansanda suke cikin lamarin, jami’an soja ma suna ciki,da kuma al’ummar makaranta. Kai har ma fa da bal’ummomin da muke da Sarakunan gargajiya da kuma duk wani abinda za’a iya amfani da shi domin samar da tsaro ga makarantu.

“Amma kuma da akwai wasu matsaloli da ya dace mu fadawa kanmu.Alal misali, a wani binciken da muka yi, mun samu wasu alkalumma da suka zarce makarantu 81,000, sai muka ce daga cikin makarantu 81,000, fiye da 60,000 hakanan suke, babu wata Katanga  a makarantun ko wasu masu gadi. A lokacin dukkan jami’an tsaro na NCSDC  63, 000 ne.

“Amma kuwa idan aka dan tunana da abubuwan da suka faru na hare- hare, ai yanzu sun  ragu, although mung a kai hare haren sosai, amma a shirye muke da tukarar ko wane lamarin daya shafi tsaro ne. Muna tuntubar juna tare da jami’an tsaro kwarai da gaske da kuma sauran masu ruwa da tsaki,domin tabbatar da dukkan matsalolin tsaro tare da kawo su hare- haren an kawo karshensu.

Babban Sakatare na Hukumar TETFund, Arc. Sonny Echono, ya nuna jin dadinsa akan irin ayyukan da NSCDC  take yi tare da wasu jami’an tsaro saboda hadin gwiwar da suke yi domin samarwa  kasa ta kasance cikin tsaro, har ila yau kuma ya tabbatar shirin kota kwana na taimako da kuma gudunmawa.

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *