Hare-haren Isra’ila sun kashe mutum 52, sun jikkata 154 a Lebanon

[ad_1]



Gwamnatin Lebanon ta ce hare-haren da Isra’ila ta kai sun kashe akalla mutane 52, yayin da 154 suka jikkata, ciki har da babban jami’in leken asiri na ƙungiyar Hezbollah.

Wannan na zuwa ne bayan wani rahoto da Ma’aikatar Lafiya ta Lebanon ta fitar tun da farko, wanda ya bayyana alƙaluman mutane 31 da suka mutu, yayin da 149 suka jikkata.

Hare-haren bama-bamai da aka kai a kudanci da gabashin Lebanon, da kuma unguwannin kudancin birnin Beirut, sun tilasta wa fiye da mutane 28,500 barin muhallansu, a cewar hukumar kula da bala’o’i da bayar da agajin gaggawa ta gwamnati.

Gwamnatin Lebanon ta haramta ayyukan Hezbollah

DW ya ruwaito cewa Gwamnatin Lebanon ta haramta ayyukan soji na ƙungiyar Hezbollah tare da neman su ajiye makamansu cikin gaggawa.

Haramta ayyukan Hezbollah na zuwa ne bayan da ƙungiyar ta harba rokoki da jirage marasa matuƙa zuwa Isra’ila a mastayin fansar kai wa Iran hari.

Wannan dai shi ne mataki mai zafi da gwamnatin Lebanon ta ɗauka a kan Hezbollah a baya-bayan nan wacce ba a taɓa ganin irinta ba, duk da cewa ƙungiyar na da wakilici a gwamnati da kuma majalisar dokoki.

Yanzu haka dakarun Isra’ila sun bayar da umarnin kwashe mutane don kawar da su daga yankunan Lebanon da dama.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *