Harin ’yan ta’adda ya hallaka direbobin tanka 15 a Mali

[ad_1]



Aƙalla direbobin tankar mai 15 ne suka rasa rayukansu a wani mummunan hari da ’yan ta’adda suka kai wa ayarin tankokin mai a yammacin ƙasar Mali a makon jiya.

Majiyoyin cikin gida sun shaida wa kamfanin dillancin labarai na AFP cewa an kai harin ne ranar Alhamis a kan babbar hanyar da ta tashi daga kan iyakar Senegal zuwa birnin Kayes, inda jami’an gwamnati suka ce an lalata tankokin mai da dama.

Wani mai gabatar da shirin rediyo a garin Diboli ya ce an ƙirga gawarwakin direbobi 15 a kusa da tankokin da aka ƙona, yayin da wani jami’in tsaro ya bayyana cewa adadin wadanda suka mutu ya kai 18.

Ya ce an bar gawarwakin a bakin hanya kusa da tankokin da aka ƙone, inda warin gawarwakin ya tilasta wa mazauna yankin fitowa domin ganin abin da ya faru har aka kai ga binne su a wurin.

Kungiyar JNIM, wacce ke da alaƙa da Al-Qaeda, ta ce ta kai wa sojojin Mali hari tsakanin Diboli da Kayes, sai dai ba ta ambaci harin kan tankokin man ba.

Sai dai wani jami’in tsaro ya bayyana cewa ‘yan ta’addan sun tsayar da direbobin ne kafin su kashe su, suna zarginsu da kai mai zuwa Bamako duk da takunkumin shige-da-fice da man da suka ƙaƙaba.

Ba kasafai aka fiye amfani da hanyar Senegal wajen safarar mai ba, kuma tuni aka dakatar da rakiyar sojoji a kan wannan hanya, bayan mayar da hankali kan hanyoyin da ke shigowa daga ƙasar Ivory Coast.

Tun daga watan Satumba, JNIM ke kai hare-hare kan tankokin mai a wani yunƙuri na daƙile harkokin man fetur da zummar durƙusar da tattalin arzikin ƙasar.

Sai dai hare-haren sun ragu a ‘yan makonnin nan, inda wannan hari ya zama mafi muni tun farkon Disamba.

Mali na fama da matsalar tsaro tun 2012, sakamakon hare-haren ‘yan ta’adda masu alaƙa da Al-Qaeda da ISIS, da kuma ‘yan bindiga.

Sai duk da alƙawarin da shugabannin mulkin soja suka yi bayan ƙwace iko a 2020 da 2021, har yanzu ba a samu nasarar daƙile ta’addanci ba.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *