Yaƙin Iran na iya ɗaukar fiye da makonni huɗu — Trump
[ad_1]
Shugaba Donald Trump ya ce yaƙin da ake yi da Iran na iya ɗaukar fiye da makonni huɗu, yana mai cewa Amurka a shirye take ta ci gaba da yaƙin idan hakan ya zama dole.
Trump ya faɗi hakan ne a cikin wani jawabi mai tsawo, inda ya sake nanata abin da ya faɗa a wata hira da jaridar Daily Mail a ranar Lahadi, cewa yaƙin na iya ɗaukar makonni huɗu zuwa biyar.
Ya ƙara da cewa, a haƙiƙa, Amurka na iya wuce wannan lokaci idan buƙatar hakan ta taso, yana mai cewa ba zai gajiya ba ko da yaƙin ya daɗe yana gudana.
Maganganun na Trump na zuwa ne a daidai lokacin da ake ci gaba da musayar hare-hare tsakanin Amurka, Isra’ila da Iran, lamarin da ke ƙara tayar da hankula a yankin Gabas ta Tsakiya.
Masu alaƙa
[ad_2]
Source link