Shugaban Syria ya yi jawabi a taron MDD karon farko cikin kusan shekaru 60

[ad_1]



Shugaban gwamnatin riƙon ƙwaryar Syria Ahmed al-Sharaa ya shaida wa babban taron Majalisar Dinkin Duniya cewa ƙasarsa ta sake ƙwato matsayinta a idon duniya.

Wannan ne karon farko cikin kusan shekaru 60 da wani shugaban Syria ya yi jawabi a taron MDD.

Al-Sharaa ya zama shugaban Siriya na farko da ya yi jawabi a Majalisar Dinkin Duniya tun bayan da Noureddine Attasi ya yi jawabi a shekara ta 1967, jim kaɗan bayan yaƙin Larabawa da Isra’ila, a lokacin da Damashka ta rasa iko da tuddan Golan wanda Isra’ila ta ƙwace a shekarar 1981.

Al Sharaa ya ce yaƙin basasa ya ɗaiɗaita Syria, amma ya alƙawarta gudanar da zaɓuka a ƙasar.

Jawabin da ya yi a taron na MDD da ke gudana a New York ya ɗauki hankalin mahalarta taron a Amurka, ƙasar da a baya ta sanya tukwicin dala miliyan 10 ga wanda ya taimaka aka kama shi.

A watan Disamban da ya gabata ne aka kawo ƙarshen mulkin kama-karya da iyalan Assad suka shafe kusan rabin ƙarni suna yi a Siriya, bayan da aka kifar da Shugaba Bashar al-Assad a wani gagarumin samame da dakarun ’yan tawaye ƙarƙashin jagorancin al-Sharaa suka kai.

Kifewar Assad ta kawo ƙarshen daular mulkin da ta mamaye Siriya na tsawon shekaru 50, tare da kawo ƙarshen yaƙin basasa da ya shafe fiye da shekaru 14 yana addabar ƙasar.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *