A shirye muke mu shafe lokaci mai tsawo muna yaƙi da Amurka — Iran

[ad_1]



Sakataren Majalisar Tsaron Iran, Ali Larijani, ya ce ƙasarsa a shirye take domin gwabza yaƙi mai tsawo idan hakan ya zama dole, a rikicin da ke ƙara ƙamari tsakaninta da Amurka.

Larijani ya bayyana hakan ne cikin wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na X, inda ya ce fiye da shekara 300 Iran ba ta taɓa tsokano yaƙi ba, kuma dakarunta ba sa shiga faɗa sai don kare kai.

“Duk abin da zai faru, za mu kare kanmu. Za mu kuma yi amfani da tarihin daularmu na tsawon shekara 6,000 don tabbatar da cewa maƙiyanmu ba za su samu nasara a kanmu ba,” in ji shi.

Tun da farko, Hukumar Tsaron Amurka ta bayyana cewa harin da Amurka ta kai wa Iran ba na dindindin ba ne.

Sakataren tsaron Amurka ya shaida wa manema labarai cewa manufar harin ita ce lalata makaman linzami na Iran, rundunar sojin ruwan ƙasar, da wasu muhimman kayayyakin soji, ba wai shiga yaƙi mai faɗi ba.

Ya ƙara da cewa Amurka za ta ci gaba da sanya ido kan halin da ake ciki, yana mai cewa duk wani mataki na gaba zai dogara ne da yadda Iran za ta mayar da martani.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *