Isra’ila ce ta kashe Khamenei ba Amurka ba — Pentagon
[ad_1]
Babban jami’in manufofin tsaro na ma’aikatar tsaron Amurka (Pentagon) ya bayyana cewa Amurka ba ta da hannu a mutuwar Jagoran Musulunci na Iran, Ayatollah Ali Khamenei, inda ya bayyana cewa harin Isra’ila ne ya yi sanadiyyar mutuwarsa.
A lokacin da yake ba da shaida hakan a gaban Kwamitin Ayyukan Soja na Majalisar Dattawa, Elbridge Colby ya bayyana cewa harin da ya kashe Khamenei da sauran manyan shugabannin Iran ba ya cikin shirin ayyukan sojin Amurka.
“Waɗannan ayyuka ne na Isra’ila,” in ji Colby, yayin da yake mayar da martani ga matsin lamba daga ’yan majalisa kan ko kifar da gwamnati na ɗaya daga cikin manufofin matakin da Amurka ta ɗauka.
Salon kalaman Colby mai natsuwa ya bambanta da na Shugaba Donald Trump, wanda ya bayyana rikicin cikin kalaman nasara da jaddadawa tun lokacin da aka fara kai hare-haren.
“Tsawon shekaru 47, gwamnatin Iran tana rera taken ‘mutuwa ga Amurka’ kuma ta gudanar da kamfen na zubar da jini da kisan kiyashi ba ƙaƙƙautawa,” in ji Trump ranar Asabar.
A wani saƙo da ya wallafa a dandalin sada zumunta, Trump ya ce Khamenei ya “kasa tserewa dabarun leƙen asirinmu da na’urorinmu na zamani masu bin sawu,” sannan ya ƙara da cewa, “ta hanyar haɗin gwiwa da Isra’ila, babu abin da shi (Khamenei) ko sauran shugabannin da aka kashe tare da shi za su iya yi.”
Wannan saɓani na kalami ya fito da wasu manyan tambayoyi game da manufofin gwamnatin Amurka a Iran.
Sakataren Wajen Amurka, Marco Rubio ya bayyana ranar Litinin cewa Washington ta ɗauki mataki ne kawai bayan ta sami labarin cewa Isra’ila na shirin kai hari, wanda hakan ke nuna cewa matakin Amurka martani ne kawai maimakon wani babban shiri da aka tsara.
“Manufofin ayyukan soja… sun mayar da hankali ne kan rage ƙarfin Jamhuriyar Musulunci ta Iran na yin amfani da ƙarfin soji kanmu, sansanoninmu, dakarunmu, da sauran su, har ma da kawayenmu da abokan hulɗarmu a yankin da ma bayansa,” in ji shi.
Ya bayyana cewa, manyan manufofinsu su ne makaman linzamin Iran — waɗanda ya ce sun ƙaru sosai — da kuma ƙarfinta na ƙera waɗannan makaman da kuma wasu sassa na dakarun ruwan Iran.
Ya kafa hujjar cewa wadannan manufofi ne “masu ma’ana kuma wadanda za a iya cimmawa.”
Masu alaƙa
[ad_2]
Source link