Ya Kamata Kasa Da Kasa Su Hada Hannu Su Kare Wayewar Kan Duniya Daga Masu Yunkurin Mayar Da Hannun Agogo Baya

[ad_1]

Yayin da yanayin ya dau zafi a yankin Gabas ta Tsakiya da ma duniya baki daya, saboda mummunan matakin Amurka da Isra’ila na farwa Iran yayin da ake tsaka da tattaunawa a tsakanin Iran da Amurka, kamar kullum, kasar Sin ta bayyana matsayarta a matsayinta na wadda ta san ya kamata. Kuma a ganina batutuwan da ta bayyana, su ne hanyoyin samun zaman lafiya da karewa da tabbatar da cikakken ’yancin kasashen duniya.

A jiya Lahadi, yayin tattaunawa ta wayar tarho tsakanin ministan harkokin wajen Sin Wang Yi da takwaransa na Rasha, Sergei Lavrov bisa bukatar Lavrov din, ministan na kasar Sin ya fayyace matsayar kasarsa dangane da batun.

Kamar yadda ya fada, ya kamata a gaggauta dakatar da kai hare-hare domin kandagarkin bazuwar rikicin. Duniya na cikin yanayi na tashin hankali. Har yanzu ana fama da rikice-rikice a sassan daban-daban daga na Rasha da Ukraine, zuwa na Sudan da yankin Gaza, inda al’ummomin duniya da ba su ji ba su gani ba, suke dandana kudarsu saboda mummunan tasirinsu. Shin wannan kadai bai isa ya sa Amurka da Isra’ila su sassauta daga amfani da karfi fa? Shin wannan yunkuri na wanzar da zaman lafiya ko kuwa na kara hargitsa duniya?

A wannan sabon zamanin da ake ciki da tarin kalubalen da dan Adam ke fuskanta, bai kamata a ce ana nuna karfi kamar zamanin mulkin mallaka da babu ’yantattun kasashe da dokokin kasa da kasa ko hukumomi masu shiga tsakani ba.

Abu na biyu da Wang Yi ya bayyana shi ne, gaggauta komawa teburin sulhu.

Mun ga yadda dukkan yake-yake da rikice-rikicen dake wakana ke komawa teburin sulhu bayan gwabza fada, lamarin dake nuna cewa, amfani da karfi ba ya haifar da da mai ido. Yanayi da al’adun kasashe sun bambanta, don haka dole a samu sabanin ra’ayi tsakanin bangarori daban-daban, amma a matsayin mutane wadanda suka mallaki hankali, kamata ya yi a rika amfani da hankali da hangen nesa, a tattauna don lalubo hanyoyin cimma yarjejeniya da hakuri da wasu batutuwa domin samun zaman lafiya da kwanciyar hankali. Diplomasiyya ta fi taka rawa a dangantakar kasa da kasa sama da fito na fito da raini da amfani da karfi.

Batu na 3 da ministan na Sin ya tabo shi ne, kasa da kasa su hada kai wajen adawa da yadda ake gaban kai wajen daukar matakai. Hakika yin gaban kai wajen daukar matakai, sam bai dace da zamanin wayewar kai da ilimi ba. Wannan salo ne na rashin wayewa, kuma ya zama wajibi kasa da kasa su hadu su yi magana da murya guda don kaucewa mayar da hannu agogo baya na ci gaban da dan adam ya samu. Muddun aka gaza yin hakan, to babu wanda zai tsira.

Hakika a matsayinta na babbar kasa da kullum take nuna hangen nesa da sanin ya kamata, kasar Sin ta gabatar da hanyoyi masu dacewa na tabbatar da zaman lafiya a duniya. Sai dai, ita kadai ba za ta iya ba. Fatan ita ce, kasa da kasa su yi nazari, su kuma yi abun da ya kamata. (Fa’iza Mustapha)

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *