An kashe mutum 11 da jikkata wasu 29 a bikin Yahudawa a Ostireliya

[ad_1]



Akalla mutanen 11 ne suka mutu, wasu 29 suka jikkata, a yayin wani hari da aka kai a bakin tekun  Bondi Beach da ke birnin Sydney na ƙasar Ostireliya.

’Yan bindiga sun kai harin ne a yayin da dubban jama’a ne suka taru a bakin teku domin halartar wani biki mai suna ‘Chanuku, kusa da tekun ‘wanda ke nuna fara shagulgulan Yahudawa na Hanukkah.

Rahotanni sun ce wani mutum da ake zargin ɗaya daga cikin masu harin ya mutu, yayin da wani kuma ke cikin mawuyacin hali a asibiti. ’Yan sanda biyu na cikin mutanen da suka jikkata.

Hukumomin Ostireliya sun bayyana lamarin a matsayin harin ta’addanci, tare da jaddada cewa an shirya shi ne domin kai wa al’ummar Yahudawa hari a ranar farko ta bukukuwan Hanukkah.

Firaministan Ostireliya, Anthony Albanese, ya yi Allah-wadai da harin, tare da cewa mummunan ta’addanci da aka aikata ya wuce tunanin ɗan adam.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *