Iran ta kai hari sansanin sojin Amurka da Birtaniya a Tsibirin Chagos
[ad_1]
Wani rahoto ya ce Iran ta harba makamai masu linzami zuwa sansanin haɗin gwiwar sojojin Amurka da Birtaniya da ke Diego Garcia a Tsibirin Chagos, cikin Tekun Indiya.
Mujallar Wall Street ce ta rawaito hakan, inda ta ce nisan da ke tsakanin Iran da tsibirin ya kai kimanin mil 2,500, wato kusan kilomita 4,000, lamarin da ke nuna yiwuwar Tehran na da makamai masu tafiyar dogon zango fiye da yadda ake zato a baya.
Rahoton ya ƙara da cewa har zuwa lokacin tattara bayanai, Ma’aikatar Tsaron Amurka Pentagon ba ta yi tsokaci kan lamarin ba.
Sai dai babu cikakken bayani kan irin ɓarnar da harin ya haddasa ko ko an samu asarar rayuka, a yayin da wasu rahotanni ke cewa makaman ba su kai inda suka nufa ba.
Harin na zuwa ne bayan Firaministan Birtaniya, Keir Starmer, ya amince Amurka ta ci gaba da amfani da sansanonin Birtaniya wajen kai hare-hare kan Iran.
Ministan harkokin wajen Iran, Abbas Araghchi, ya yi gargaɗin cewa rayukan ‘yan Birtaniya na cikin haɗari, yana mai cewa ƙasarsa za ta yi amfani da haƙƙinta na kare kanta.
A halin yanzu, gwamnatin Birtaniya na fuskantar suka daga jam’iyyun adawa kan matakin bai wa Amurka damar amfani da sansanoninta, yayin da ake sa ran za a tattauna batun a wani taron gaggawa na tsaro da ake yi wa laƙabi da Cobra.
Masu alaƙa
[ad_2]
Source link