An ceto wata mata da ta faɗa rijiya a Kano
[ad_1]
Hukumar Kashe Gobara ta Jihar Kano ta ceto wata mata ’yar shekara 23 mai suna Ladidi Muhammad Sani, bayan ta faɗa cikin wata rijiya a unguwar Gurungawa da ke Ƙaramar Hukumar Kumbotso a safiyar Talata.
Hukumar ta bayyana cewa ta samu kiran gaggawa da misalin ƙarfe 12:25 na dare, wanda hakan ya sa aka gaggauta tura tawagar ceto daga hedikwatar hukumar zuwa inda lamarin ya faru.
A cikin wata sanarwa da kakakin hukumar, Saminu Yusif Abdullahi, ya sanya wa hannu, Daraktan Hukumar Kashe Gobara ta Jihar Kano, Alhaji Sani Anas, ya ce an samu nasarar ceto matashiyar lafiya lau, inda daga bisani aka miƙa ta ga mahaifinta, Abdullahi Sani.
Sanarwar ta ƙara da cewa har yanzu ana ci gaba da bincike domin gano musabbabin faɗawarta cikin rijiyar.
Hukumar ta buƙaci al’umma da su ɗauki matakan kariya da suka dace, musamman a kusa da rijiyoyin da ke buɗe domin kauce wa afkuwar irin wannan lamari a nan gaba.
Masu alaƙa
[ad_2]
Source link