Taron APEC Na 2026 Da Za A Shirya A Kasar Sin Zai Bude Sabon Babin Na Gina Al’ummar Bai Daya Ta Asiya-Pasifik
[ad_1]
Jiya Asabar 1 ga watan nan na Nuwamba, a birin Gyeongju na kasar Koriya ta Kudu, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya halarci wani bangare na kwarya-kwaryar taron shugabannin APEC na karo na 32, inda ya karbi bakuncin taron daga mai masaukin baki na wannan karo, ya kuma sanar da cewa, kasar Sin za ta karbi bakuncin kwarya-kwaryar taron shugabannin APEC karo na 33, wanda ake sa ran gudanarwa a watan Nuwamban shekara mai zuwa, a birin Shenzhen na lardin Guangdong dake kudancin kasar.
Wannan shi ne karo na uku da Sin za ta karbi bakuncin taron APEC, bayan na shekarun 2001 da 2014. Shugaba Xi ya jaddada cewa, kasarsa na son amfani da wannan dama mai kyau, don hada kai tare da bangarori daban daban masu ruwa da tsaki, wajen gina al’umma mai kyakkyawar makoma ga yankin Asiya da Pasific, kana da inganta ci gaba da wadatar shiyyar.
A safiyar ranar Juma’a 31 ga watan Oktoban da ya gabata, aka gudanar da taron mataki na farko, na kwarya-kwaryar taron shugabannin kungiyar APEC karo na 32, a cibiyar taro ta Hwabaek ta Gyeongju (Hwabaek ICC) na kasar Koriya ta Kudu. An lura da cewa a wannan taro na APEC, shugaba Xi ya sha ambaton alakar tattalin arzikin Sin da ta duniya. “Kasar Sin ba za ta rufe kofarta ga waje ba, sai dai ma ta kara budewa” “Tafiya tare da Sin, tafiya ce tare da dama. Amincewa da Sin amincewa ne da makoma. Zuba jari a Sin, zuba jari ne don gobe.”…Wadannan kamalan da shugaba Xi ya yi sun nuna wa kasashen duniya tsayayyiyar niyyar kasarsa, ta inganta raya tattalin arzikin duniya mai budewa.
Bayan an mika damar karbar bakuncin taron kungiyar APEC, kasashen duniya sun soma zura ido kan kasar Sin. Ana sa ran cewa, taron APEC da za a gudanar a Shenzhen, zai kara habaka hadin gwiwa, da samun ci gaba, da wadata tare a shiyyar, kana zai shaida yadda kasar Sin ke kara samar da sabbin damammaki ga yankin Asiya da Pasifik, bisa ga sabbin nasarorin da take samu ta hanyar zamanantarwa irin ta kasar Sin. (Mai fassara Bilkisu Xin)
[ad_2]
Source link