Gwamnatin Tarayya Ta Dawo Da ‘Yan Nijeriya 1,231 Daga Jamhuriyar Nijar A Mako Daya

[ad_1]

Gwamnatin tarayyar Nijeriya ta samu nasarar dawo da wani karin rukuni na ‘yan gudun hijira mutum 523 da suka makale a Niamey na Jamhuriyar Nijar, inda jimlar wadanda aka dawo da su ya kai 1,231 a cikin mako guda.

An karbi wadanda aka dawo da su ne a Kano ranar Lahadi, 29 ga Maris, 2026, karkashin kulawar hukumar kula da ‘yan gudun hijira da matafiya da masu tabun hankali ta kasa (NCFRMI).

  • Kungiyar Jama’atu Ta Yi Tir Da Kashe-kashen Da Suka Auku A Jos
  • Ba Za A Iya Daidaita Batun Mashigin Hormuz Ba Har Sai An Kawo Karshen Yaki

Da yake jawabi kan lamarin a madadin kwamishinan hukumar NCFRMI, Hon. Tijjani Aliyu Ahmed, shugabar hukumar ta Jihar Kano, Hajiya Lubah Liman, ta bayyana wannan aikin a matsayin fitar da ‘yan Nijeriya da suka makale daga Jamhuriyar Nijar bisa bukatar kansu.

A cewarta, gwamnatin tarayya ce ta saukaka dawo da su kasarsu karkashin jagorancin Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu da mataimakin shugaba kasa, Kashim Shettima, ta hanyar ma’aikatar harkokin waje tare da hadin gwiwar hukumar.

“Wannan sabon aikin ya biyo bayan wani rukuni na baya na ‘yan gudun hijira guda 708 da aka karba a ranar Litinin, 23 ga Maris, 2026. Tare da isowar rukuni na biyu, jimillar ‘yan Nijeriya da aka dawo da su daga Jamhuriyar Nijar a cikin wannan lokaci yanzu sun kai 1,231,” in ji ta.

Bayanan dawowar mutane sun nuna cewa rukunin ya kunshi maza 345, ciki har da mayan maza 267, yara maza 78 da mata 178, wanda ya hada da mata manya 104 da ‘yan mata 74.

Wadanda aka dawo da su sun bi ta hanyoyi da ke sassa daban-daban na kasar, ciki har da Kano, Jigawa, Filato, Katsina, Taraba, Inugu, Ebonyi, Legas, Ribas, Borno, Zamfara, Bauchi, da sauransu.

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *