Ya Kamata Sin Da Amurka Su Kaucewa Takara Mai Hadari

[ad_1]

Ministan kula da cinikayya na kasar Sin Wang Wentao, ya ce ya kamata Sin da Amurka su karfafa hadin gwiwa mai ma’ana da kaucewa takara mai hadari.

Wang Wentao ya bayyana haka ne yayin ganawarsa da wakilin tattauna harkokin cinikayya na Amurka, Jamieson Greer a jiya Alhamis, a gefen taro na 14 na ministocin kasashen hukumar kula da cinikayya ta duniya (WTO) dake gudana a Yaounden Kamaru.

Bangarorin biyu sun yi tattaunawa mai zurfi kan dangantakar tattalin arziki da cinikayya tsakanin kasashensu, da tsarin cudanyar kasa da kasa da hadin gwiwar tattalin arziki.

Ministan na Sin ya kara da cewa, ya kamata dangantakar cinikayya da tattalin arziki ta ci gaba da zama karfi mai ingiza huldar kasashen, maimakon zama tsaiko ko musababbin rikici.

Ya kuma nanata cewa a shirye Sin take ta karfafa tsarin cudanyar bangarori da hadin gwiwar tattalin arziki da cinikayya da Amurka, da hada hannu wajen ingiza gyare-gyare a WTO da taimakawa taron ministoci na 14 na WTO wajen samun sakamako mai kyau da goyon bayan kyawawan sakamakon tarukan kungiyoyin APEC da na G20.

Yayin ganawar, Wang Wentao ya bayyana damuwar kasarsa game da sashen bincike na 301 da Amurka ta kaddamar kan kasashe da dama, ciki har da Sin, kan abun da ta kira samar da kayayyaki fiye da kima da kuma haramta cinikin kayayyaki saboda zargin da take yi ana tilasta wa mutane ayyukan kwadago. (Mai Fassara: Fa’iza Mustapha)

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *