Gobara ta cinye shaguna a Tashar Motoci ta Jabi a Abuja

[ad_1]



Ana fargabar shaguna kimanin 100 sun jone bayan tashin gobara da tsakar dare a Babbar Tashar Motoci ta Jabi da ke shiyyar Iraki a Abuja, a safiyar Asabar.

Da talatainin dare kafin asubahi gobarar ta tashi inda ta cinye akasarin shagunan wucin gadi na masu sayar da kayan hannu kayan waya da dangoginsu a tsakanin Babbar Kofar farko da Kofa ta Biyu da ke tashar motocin.

Wani ɗan kasuwar ya ce da misalin ƙarfe 3.30 na dare wutar ta tashi, amma ba a kai ga gano musabbinta ba.

Tun da misalin ƙarfe 4 na Asuba ’yan kasuwa da ’yan kwana-kwaba suka yi dafifi a kasuwar domin kashe wutar.

A halin yanzu ’yan Kasuwar na ƙoƙarin kwashe kayayyakin da gobarar ba ta shafa ba.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *