Jami’an Tsaro 6 Sun Rasu Yayin Da Aka Daƙile Harin ’Yan Ta’adda A Zamfara

[ad_1]

Rundunar tsaro karkashin Operation FANSAN YAMMA ta daƙile wani harin ’yan ta’adda a kan hanyar Bingi–Kekun Waje–Gusau a Jihar Zamfara.

Duk da daƙile harin, sojoji biyar da ɗan sanda ɗaya sun rasa rayukansu a yayin artabun.

  • Jama’a Sun Nuna Rashin Gamsuwa Da Donald Trump Yayin Da Ya Cika Shekara Guda a Wa’adin Mulkinsa
  • Mataimakin Ministan Wajen Sin: Nuna Karfin Tuwo Ba Abun Da Zai Haifar Sai Koma Baya

A cewar sanarwar rundunar, harin kwanton-ɓaunan ya biyo bayan wasu manyan ayyukan soji da aka gudanar tsakanin 17 zuwa 19 ga watan Janairu domin lalata maɓoyar ’yan ta’adda a yankunan Birnin Magaji da Anka.

A yayin waɗannan ayyuka, an kama mutane uku da ake zargi, yayin da aka kashe ’yan ta’adda huɗu.

Jami’an tsaron sun kuma ƙwato makamai, alburusai, na’urorin sadarwa, da babura.

Lokacin da sojoji suka kai ɗauki bayan kiran gaggawa a Gidan Wagni, ’yan ta’addan sun buɗe musu wuta.

Duk da haka, sojojin sun mayar da martani tare da kare al’ummomin da ke yankin.

Daga bisani, ƙarin sojoji sun isa wajen, lamarin da ya tilasta wa ’yan ta’addan tserewa.

Rahotanni sun nuna cewa wani ƙasurgumin shugaban ’yan bindiga mai suna Janwuya da mataimakinsa sun jikkata sosai.

A halin yanzu, jami’an tsaro na ci gaba da bin sahun ’yan ta’addan tare da haɗin gwiwar ’yan banga.

Rundunar ta tabbatar wa jama’a cewa tana ci gaba da tsaurara matakan tsaro, tare da roƙon al’umma su riƙa ba da sahihin bayanai ga hukumomin tsaro.

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *