’Yan Najeriya sun sha barasar tiriliyan N1.54 a wata 9
[ad_1]
Manyan kamfanonin giya a Najeriya sun samar da jimillar kuɗaɗen shiga sama da tiriliyan N1.54 daga sayar da giya da sauran abin sha marasa giya cikin watanni tara na farkon shekarar 2025.
Alƙaluman dai na nuna adadin kuɗin da ’yan Najeriya suka kashe wajen sayen kayayyakin giya a wannan lokaci.
A cewar bayanan kuɗi da ba a tantance ba na kamfanonin giya na Nigerian Breweries, International Breweries, da Champion Breweries Plc na watanni tara da suka ƙare a ranar 30 ga watan Satumba, 2025, kamfanonin sun samu babban ci gaba ta sayar da giya.
Jimillar kuɗaɗen shiga na kamfanonin uku ya kai N1.54 tiriliyan, inda Nigerian Breweries Plc ta fi da yawa.
Masana sun ce waɗannan alkaluman sun nuna ƙarfin kasuwar giya ta Najeriya, wadda ke ci gaba da samun tagomashi daga aminci ga alamu da kuma hanyoyin rarrabawa duk da tsadar sarrafawa da matsalolin tattalin arziki.
A cikin sharhinsa kan halayyar masu ta’ammali da giya, Shugaban Sashen Kimanta Hukumomin Kuɗi na Agusto & Co., Ayokunle Olubunmi, ya ce kasuwar na fuskantar sauyi a hankali kan yadda ake kashe kuɗi, inda wasu masu amfani ke rage shan giya, abin da ke shafar dabarun da kamfanonin giya ke ɗauka.
Masu alaƙa
[ad_2]
Source link