Darussa Daga Ramadan Na 12: Ƙarfafa Alaƙa Da Alƙur’ani A Ramalana
[ad_1]
A cikin watan Ramalana muna koyon ƙarfafa alaƙarmu da Alƙur’ani mai girma. Ta yaya ba za mu ƙarfafa wannan alaƙa ba, alhali Allah Maɗaukaki Ya zaɓi wannan wata domin saukar da littafinsa mafi girma? Idan lokaci ya samu daraja saboda Alƙur’ani, to ya dace mu ɗaukaka rayuwarmu ta hanyar komawa gare shi.
Allah Mai Tsarki Ya ce a Suratul Baƙara aya ta (185): “Watan Ramalana shi ne aka saukar da Alƙur’ani a cikinsa, shiriya ne ga mutane, kuma ayoyi ne bayyanannu na shiriya, kuma mai rarrabewa ne tsakanin ƙarya da gaskiya”
- Darussa Daga Ramadan Na 11: Sauƙi Da Sassauci A Shari’a
- Darussa Daga Ramadan Na 10: Zumunci Da Tausayi
Wannan aya ta nuna mana darajar Ramalana da kuma darajar Alƙur’ani. Alƙur’ani shiriya ne, yana haskaka duhun zuciya. Bayyanannun hujjoji ne, da suke tabbatar da gaskiya. Kuma Mai rarrabewa ne tsakanin gaskiya da ƙarya, da halal da haram, da kuma haske da duhu.
Ramalana wata ne da zukata suke natsuwa, sha’awoyi suke rauni, ruhi kuma yake kusantar Allah. Saboda haka karatun Alƙur’ani a wannan wata yana da wani zaƙi na musamman. Ka ga mutane suna ƙoƙarin kammala shi sau ɗaya ko fiye, suna sauraron tafsiri, suna yawaita tadabburi.
Wannan yanayi yana nuna cewa zuciya tana buƙatar Alƙur’ani fiye da komai. Sai dai wata tambaya ita ce: mene ne ya sa wannan kusanci da Alƙur’ani yake raguwa bayan Ramalana? Ina ma za mu lazimci karatunsa tsawon shekara kamar yadda muke lazimtar karantawa a cikin Ramalana. Domin Alƙur’ani ba na wata guda ba ne; jagora ne na rayuwa baki ɗaya, amma watan Ramalana na daban ne wannan shi ne dalilin.
Ƙarfafa alaƙa da Alƙur’ani yana nufin abubuwa uku:
1. Karatunsa akai-akai, ko da aya kaɗan ce a rana, amma a dawwama ana yi ba tare da tsallake ba.
2. Tadabburi da fahimta, watau tunani a kan ma’anoni da saƙonnin da yake ɗauke da su.
3. Aiwatarwa ta fuskar aiki da shi, watau a mayar da koyarwarsa aiki a rayuwa. Domin Alƙur’ani ba a saukar da shi domin a karanta shi kawai ba, sai domin a rayu da shi. Idan muka karanta shi ba tare da aiki da shi ba, mun rasa wani ɓangare na hikimar saukar da shi.
Ramalana makaranta ce ta komawa ga Alƙur’ani. Idan muka fita daga wannan wata da alƙawarin cewa ba za mu rabu da littafin Allah ba, to mun samu riba mai girma. Domin duk wanda ya riƙe Alƙur’ani, Alƙur’ani zai ɗaukaka shi.
Allah Ya sanya Alƙur’ani ya zama hasken zukatanmu, ya zama maganin damuwarmu, ya zama jagoran rayuwarmu a duniya da Lahira. Ya sa mu zama daga cikin mutanen Alƙur’ani waɗanda suke mutanensa na musamman. Amin.
Abu Razina Nuhu Ubale Ibrahim Paki
[ad_2]
Source link