Gwamnonin Arewa Sun Yaba Da Ci Gaban Da Tinubu Ya Samar A Yankin

[ad_1]

Shugaban Kungiyar Gwamnonin Jihohin Arewa (NSGF), kuma Gwamnan Jihar Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya, ya ce; sauye-sauyen da Shugaba Bola Tinubu ya yi, na iya zama kalubale, amma suna kan kafa wani harsashin na ci gaba.

Da yake jaddada goyon bayan taron ga Tinubu, Inuwa ya yaba wa shugaban kasa kan jagorancinsa na kawo sauyi, yayin da ya cika shekara 74.

  • Shettima Ya Nemi Hadin Kan Kafafen Yada Labaru Domin Samar Da Ci Gaba
  • Mutane Da Dama Sun Jikkata A Rikicin ‘Yan Daba A Kano

A cikin wata sanarwa da babban daraktan yada labarai na gidan gwamnatin Gombe, Ismaila Uba Misilli ya fitar a ranar Lahadin da ta gabata, gwamnan, wanda yake magana a madadin takwarorinsa, ya bayyana jagorancin shugaba Tinubu a matsayin jajirtacce da kuma jigon tabbatar da dorewar kwanciyar hankali da sauye-sauyen tattalin arzikin Nijeriya.

Gwamna Inuwa, ya bayyana cewa; tun bayan hawansa karagar mulki, shugaban ya nuna jajircewa wajen aiwatar da sauye-sauye masu ma’ana da nufin sake farfado da tattalin arzikin kasa da kuma karfafa muhimman cibiyoyi.

Haka zalika, ya amince da cewa; duk da cewa sauye-sauyen sun zo da wasu kalubale da sadaukarwa, amma matakai ne masu muhimmanci na gina kyakkyawar makoma mai dorewa da wadata ga ‘yan Nijeriya.

A cewarsa, shirin ‘Renewed Hope Agenda’ na shugaban kasar, ya ci gaba da sake farfado da amincewa a tsakanin ‘yan kasa tare da kafa wata hanya mai kyau, don ci gaba mai dorewa da samun cikakken hadin kai na kasa.

Shugaban ya kuma jaddada cewa, Jihar Gombe tare da hadin gwiwar sauran Jihohin Arewa, sun ci gaba da jajircewa wajen ganin an samu nasarar aiwatar da manufofi da shirye-shiryen shugaban kasa.

“Sauye-sauyen da shugaban kasa ya dauka na kawo ci gaba, na nuni da jagorancin da ke tattare da yakini da kuma burin tabbatar da kyakkyawar makoma ga al’ummar kasar. Koda-yake akwai kalubale, wadannan sauye-sauyen sun riga sun kafa tushen ci gaba mai dorewa,” in ji shi.

Kazalika, ya kuma kara jaddada goyon bayan hadin gwiwar gwamnonin Arewa, don ci gaba da aiwatar da ajandar kawo sauyi ga shugaban kasa fiye da yadda ake gudanar da mulki a halin yanzu.

“Mu a Jihar Gombe tare da takwarorinmu na kungiyar gwamnonin jihohin Arewa, muna godiya da goyon bayan da kuke bai wa gwamnatocin kananan hukumomi da tsarin tafiyar da harkokin mulki na kasa baki-daya, mun tsaya tsayin daka tare da ku, muna kara jaddada goyon bayanmu ga shugabancinku da hangen nesa yanzu da kuma nan gaba.

Gwamna Inuwa, ya kuma yi addu’ar Allah ya kara masa lafiya da nisan kwana.

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *