Yadda Yaƙin Basasar Nijeriya ya kasance — Soja ɗan shekara 106

[ad_1]



Wesley Tafida mai shekara 106 yana daga cikin ragowar tsofaffin ’yan matan jiya a Nijeriya da suka yi aiki da turawan mulkin mallaka kuma suka halarci Yaƙin Duniya na Biyu.

Dattijon, wanda a halin yanzu yake gidansa da ke garin Jalingo, hedikwatar Jihar Taraba ya shiga aiki a Rundunar Sojin Nijeriya a shekarar 1963, inda ya yi ritaya bayan ya kai matsayin RSM.

Haka kuma ya samar da iri a gidan soja, domin kuwa daga cikin ’ya’yansa akwai wanda ya gaje shi a aikin soja—Manjo-Janar HT Wesley mai ritaya—wanda sai da ya kai matakin Janar kafin ya yi titaya daga gidan soja,

RSM Wesley Tafida yana da shekara uku a gidan soja aka yi juyin mulki na farko da aka kashe shugabannin Nijeriya na farko irin su Fira Minista Alhaji Abubakar Tafawa Ɓalewa, da Firimiyan Jihar Arewa, Alhaji Ahmadu Bello Sardauna da sauran takwarorinsu.

Bayan shekara 60 da ƙazamain juyin, wanda ya kai ka jefa Nijeriya a cikin yaƙin basasa, RSM, wanda yake matashin soja a lokacin, ya ba labarin abin da ya shaida a lokacin yaƙin.

A wata ganawa ta musamman da walikinmu ya yi da shi a gidansa, albarkacin zagayowar Ranar Tunawa da ’Yan Maza Jiya na shekarar 2026, RSM Wesley Tafida, ya bayyana cewa aikin soja aiki ne na sayar da rai tare da sadaukar da kai domin kare martaba ƙasa.

Dalilin shigarsa aikin soja

Dattijon ya bayyana cewa kishin ƙasa ne ya sa ya shiga aikin soja a shekarar 1963 bayan yayi aiki da turawan mulkin mallaka na tsawon shekaru.

Ya ce yana cikin matasan da a wancan lokacin suka shiga aikin soja tun ana mulkin farar hula a jamhuriya ta farko, inda ya shiga makarantar koras da kuratan sojoji (Depot) da ke Zariya a shekarar 1963 inda ya samu horo na watanni bakwai.

Bayan ya kammala samun horo Depot, a shekarar 1964 sai aka tura shi zuwa Bataliyan Soja ta 2 da ke garin Abeokuta a tsohuwar Jihar Yamma.

Shekara daya bayan nan, a shekarar 1965 kuma aka yi masa sauyin wurin aiki zuwa Babban

Barikin Soja da ke Ikeja, a Jihar Legas. Yana aiki soja a barikin soja da ke Ikeja ne, da shekara ta zagayo, akayi juyin mulkin na shekarar 1966.

Yaƙin basasar Nijerya

RSM Wesley ya ce bayan ɓarkewar yaƙin basasa ne a cikin shekarar 1967 aka tura su fagen fama tare da sauran sojojin Nijeriya domin yaƙar ’yan tawayen Biyafara da ke neman ɓallewa daga Nijeriya.

Inda aka fara tura su a lokacin yaƙin shi ne garin Makurɗi, daga nan kuma suka shafe shekaru uku suna fafatawa tsakanin su sojojin Nijeriya da ’yan tawaye Biyafara.

A yayin yaƙin basasar, Wesley Tafida, ya yi aiki da shahararrun manyan sojojin kasar Nan, irin su Janar Martin Adamu da Janar Muhammadu Buhari da Kanar Adekunle da sauransu a fagen yaƙi.

Ya ce da shi aka fafata yakin a daukancin Mafindi da kuma yawanci inda aka kara tsakanin sojoji gwamnati da ’yan tawayen Biyafara waɗanda ke biyayya ga Chukwuemeka Odumegwu Ojukwu.

Ya bayyana cewa ba zai manta umarnin da Shugaban Ƙasa na mulkin soja a lokacin, Janar Yakubu Gowon ya bai wa sojojin Nijeriya waɗanda ke fagen yaƙi ba.

Kudin dokokin yaƙin da Gowon ya ba wa sojojin sun gargaɗi sojojin Nijeriya kan harbin mace da tsoffi da kuma kananan ƙara. Amma dokar ta bai wa sojojin damar harbin mace wadda take ɗauke da makami ko kuma yaro wanda ke ɗauke da bindiga, domin su ma sojojin na Nijeriya su kare kansu daga abokan gaba.

Ya ce ba zai manta da irin halaye na gari da ɗa’a tare kishin ƙasa da ya gani ba a wurin marigayi Janar Muhammadu Buhari a fagen yaƙi, kasancewar ya yi yaƙi a ƙarƙashin shi Janar Muhammadu Buhari da kanal Martin Adamu.

Bayan yaƙin Basasa

Bayan kammala yaƙi, a shekarar 1970 aka sake tura Wesley Tafida Babban Barikin Soja da ke Ikeja inda ya ci gaba da aikin soja har zuwa Shekarar 1975 lokacin da aka kashe shugaban kasa Janar Murtala a wani yunƙurin juyin mulki da aka daƙile.

Ya ce a wannan lokacin ne aka tura shi ƙarƙashin Janar T Y Danjuma inda ya yi aiki da shi a ofishinsa da ke lkoyi a Jihar Legas.

A lokacin wannan juyin mulkin wanda aka dawile, shi ne ke lura da sojojin da aka tura babban fili da ƙaramin filin jirgin sama na Ikko da Tashar Jirgin Ruwa da ke Ikko (Apapa Port) da kuma kan iyakar da Nijeriya da ƙasar Jamhuriyar Benin.

RSM Wesley ya bayyana cewa daga nan kuma a shekarar 1980 aka tura shi Makarantar Horar da Kuratan SoJoji da ke Zariya a matsayin Mai Koya wa kuratan Sojoji Aikin Soja.

Bambancin horon sojoji a jiya da yau

Ya ce har yanzu ana baiwa sojoji horo mai kyau, duk da cewa ba za a haɗa irin horon da suka samu a wancan lokacin da na yanzu ba.

Dalilin haka a cewarsu, shi ne canjin zamani. Sannan kuma masu shiga aikin soja na da yawa a yanzu idan aka kwatanta da shekaru baya saboda yawan al’ummar Nijeriya sun karu sosai yanzu.

RSM Wesley, ya ce Allah Ya kare shi har aka gama yaƙi bai taɓa

samun ko da raunin harbul ba, duk da cewa shi ne ke ɗauke da babbar bindiga mai jigida.

RSM Wesley Tafida (sanye da fararen kaya) a lokacin da Kwamandan Bitget na 6 na Rundunar Sojin Nijeriya, Birgediya Kingsley Uwa, ya kai masa ziyara a gidansa da ke Jalingo, Jihar Taraba.

Ɗaya tamkar da dubu

Ya bayyana cewa tun kafin ya shiga aikin soja baya shan giya kuma har ya yi aikin gama, har a bakin yaƙi bai taɓa sha ba, har ya yi ritaya a shekarar 1989.

Kusan ɗaukacin waɗanda suka shiga aikin soja a tare a shekarar 1963 da tsararrakinsa waɗanda suka tashi tare a garin Jen da ke Ƙaramar Hukumar Karim-Lamiɗo a Jihar Taraba duk sun mutu.

RSM Wesley, ya nuna damuwarsa kan yadda cin hanci ya yi yawa a ƙasar ta yadda waɗanda aka ba su amanar shugabanci suke sace dukiyar ƙasa domin amfanin kansu da na iyalansu.

Ya ce kuma bisa yadda wasu sojojin suka sadaukar da ransu suka shiga fagen fama aka murƙushe ’yan tawaye ba su sami kuɗaɗen barin aikin ba.

Don haka ya ba da shawarar a gudanar da bincike domin a gano irin waɗannan tsoffin sojojin domin a taikama masu.

RSM Wesley, yana da ’ya’ya tara da jikoki goma sha huɗu, cikin ’ya’yansa har da Manjo-Janar HT Wesley mai ritaya.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *