El-Rufai zai ci gaba da zama a tsare har zuwa 14 ga Afrilu

[ad_1]



Babbar Kotun Tarayya da ke Jihar Kaduna, ta ɗage sauraron buƙatar bayar da belin da tsohon Gwamnan Jihar, Nasir Ahmad El-Rufai, ya shigar zuwa ranar 14 ga watan Afrilu.

Alƙalin kotun, Rilwanu Aikawa, ya sanya ranar ne bayan ya saurari hujjoji daga lauyoyin El-Rufai da kuma masu gabatar da ƙara a ranar Laraba.

Hukumar ICPC ta gurfanar da El-Rufai a gaban kotu kan tuhume-tuhume guda 10, ciki har da zargin karkatar da kadarorin gwamnati da kuma almundahanar kuɗaɗe.

Ya musanta dukkanin tuhume-tuhumen da ake masa.

Kotun ta bayar da umarnin a ci gaba da tsare shi a hannun ICPC har zuwa ranar da za a saurari buƙatar bayar da belinsa, wato 14 ga watan Afrilu.

El-Rufai, ya isa harabar kotun da misalin ƙarfe 9 na safe cikin wata mota ƙirar Hilux tare da jami’an tsaro.

Ya sanya babbar riga fara da hula, kuma ya shiga kotun ba tare da nuna wata damuwa a fuskarsa ba.

Bayan kammala zaman kotun, ɗaya daga cikin lauyoyinsa, Ubong Akpan, ya tabbatar da ɗage shari’ar, yana mai cewa babban lauyan tawagar El-Rufai zai yi magana da manema labarai daga baya.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *