Komawar Kwankwaso ADC, Zai Jawo Hankalin Manyan ‘Yan Siyasa Zuwa Jam’iyyar

[ad_1]

Kakakin tafiyar Kwankwasiyya, Habibu Mohammad, ya bayyana cewa jam’iyyar NNPP a Jihar Kano ta mutu a zahiri, bayan ficewar tsohon dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar, Rabiu Musa Kwankwaso.

Kwankwaso ya fice daga NNPP a ranar 29 ga Maris, 2026, sannan ya koma jam’iyyar ADC a ranar 30 ga Maris, 2026.

  • Taron APC: Kansilolin Kebbi Biyu Sun Mutu Da Wani Mashawarcin Gwamna A Abuja
  • Harin Filato: JNI Ta Tabbatar Da Kashe Mambobinta 4, 10 Sun Ɓace

Da yake magana a gidan talabijin na Arise TV, Mohammad ya ce: “Duk wanda ya san siyasar Kano ya san cewa, babu wani abu NNPP face Kwankwaso, don haka ficewarsa daga NNPP kai tsaye na nufin jam’iyyar ta mutu a Kano, kuma watakila ma ba Kano kadai ba; ana iya kallonta a matsayin wadda ta mutu a fadin kasa baki daya.

“Game da tasirin Kwankwaso a ADC yanzu—kamar yadda yake da tasiri ne a NNPP a Kano, yanzu haka za a rika kallon Kwankwaso a matsayin ADC a Jihar Kano,” in ji shi.

Sai dai Mohammad ya kara da cewa, komawar Kwankwaso zuwa ADC zai jawo hankalin ‘yan siyasa daga jihohin makwabta, lamarin da zai karfafa jam’iyyar a matakin jiha da na kasa, gabanin zaben shekarar 2027.

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *