Mataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Abuja Bayan Ziyarar Guinea Da Switzerland
Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya dawo birnin Abuja bayan kammala wata ziyarar diflomasiyya da tattalin arziƙi ta tsawon mako guda zuwa Guinea-Conakry da kuma Switzerland, inda ya bayyana cewa Nijeriya ta dawo sahun gaba a tattaunawar manufofin tattalin arziƙi na duniya da na yankin.
A cewar wata sanarwa da mai taimaka masa kan harkokin yaɗa labarai, Stanley Nkwocha, ya bayyana cewa Shettima ya sauka a Filin Jirgin Sama na Nnamdi Azikiwe a ranar Asabar, bayan ya wakilci Shugaba Bola Tinubu a bikin rantsar da Shugaban Ƙasar Guinea, Mamadi Doumbouya, tare da jagorantar tawagar Nijeriya zuwa taron shekara-shekara karo na 56 na Dandalin Tattalin Arziƙin Duniya (WEF) da aka gudanar a Davos, Switzerland.
- Me Ya Sa Masu Koyarwa ‘Yan Asalin Ingila Ba Sa Iya Lashe Kofin Premier?
- Shettima Ya Ce Zuba Jari A Ɓangaren Ilimi Ba Caca Ba Ce
Shettima ya ce wannan ziyara na daga cikin ƙudirin Nijeriya na ƙarfafa haɗin kai a yankin Yammacin Afirka da kuma sake fasalin tattalin arziƙin ƙasa ƙarƙashin ajandar “Sabunta Fata” ta Shugaba Tinubu. Ya ƙara da cewa halartar bikin rantsar da Shugaba Doumbouya ya sake jaddada rawar jagorancin Nijeriya a ECOWAS da buɗe sabbin hanyoyin haɗin gwuiwa a fannonin noma da masana’antu.
Daga Guinea, Mataimakin Shugaban Ƙasar ya tafi Davos inda ya jagoranci tawagar Nijeriya a taron WEF 2026. Daga cikin muhimman abubuwan da suka faru akwai ƙaddamar da “Nigeria House Davos,” wato katafaren baje kolin Nijeriya na farko a dandalin Davos, wanda aka tsara domin jawo masu zuba jari a fannonin ma’adinai, da noma da tattalin arziƙin zamani a fannin dijital.
A wani taro na musamman kan batun tsaron abinci, Shettima ya bayyana sabon tsarin Nijeriya kan wadatar abinci, yana mai bayyana noma a matsayin ginshiƙin tsaron ƙasa da daidaiton tattalin arziƙi. Ya kuma shaida wa masu zuba jari cewa alamomin tattalin arziƙin Nijeriya na farfaɗowa, inda ya yi hasashen bunƙasar GDP da kuma raguwar hauhawar farashi, tare da nuna cewa ƙasar na gab da zama mai fitar da man fetur da aka tace, tare da ƙara fitar da sauran kaya da ma’aikatan fasahar dijital zuwa kasuwannin duniya.