’Yan bindiga sun kashe mutum 2 a wani sabon hari a Binuwai
[ad_1]
Aƙalla mutum biyu ne suka rasu a wani sabon hari da ’yan bindiga suka kai wasu yankuna biyu da ke Ƙaramar Hukumar Apa ta Jihar Binuwai.
Mazauna yankin sun ce ’yan bindigar sun kai wa al’ummar Akpete hari da yammacin ranar Juma’a, inda suka kashe mutum biyu; Matthew Ochanga da Isaac Adanu.
Wasu mutane da dama kuma sun jikkata.
A lokaci guda, maharan sun kuma kai wa al’ummar Edikwu hari, amma jami’an tsaro tare da matasan yankin sun daƙile harin tare da fatattakar su.
Shugaban Ƙaramar Hukumar Apa, Adams Ocheiga, ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce an ƙara tsaurara matakan tsaro a yankin domin hana sake aukuwar harin.
’Yan sanda ma sun tabbatar da lamarin, inda suka ce jami’an Rundunar Rapid Response Squad sun daƙile harin da aka kai Edikwu, kuma a halin yanzu yankin na cikin kwanciyar hankali.
Sun kuma ƙara da cewa ana ci gaba da gyaran wata gada da aka lalata a baya, a ƙarƙashin tsauraran matakan tsaro.
Masu alaƙa
[ad_2]
Source link