Sulhu da ’yan bindiga ya zame mana alƙaƙai — Zamfarawa

[ad_1]



Sulhu da ’yan bindiga ya zame mana alƙaƙai — Zamfarawa

Daga Abdullahi Abdulrahman Chakwa, Gusau

Al’ummar kauyen Madira da ke cikin Karamar Hukumar Kaura Namoda, Jihar Zamfara, sun koka kan yadda sulhun da suka yi da ’yan bindiga ya zamar musu alakakai, tare da haddasa tsamin dangantaka tsakaninsu da mutanen kauyen Nkaba. Lamarin ya haddasa salwantar rayuka da jikkata wasu.

Aisha Usman Kaura, ’yar asalin Madira, ta zargi mutanen Nkaba da kashe kaninta tare da jikkata wani. Ta ce mutanen Nkaba sun tsani mutanen Madira saboda kawai sun nemi mafita ta hanyar sulhu da ’yan bindiga domin su tsira da rayukansu.

> “Mun yi sulhu da ’yan bindiga domin mu tsira da rayukanmu bayan matsanancin halin da muka shiga saboda matsin lambar ’yan bindiga. Gwamnati ta kasa kawo mana dauki, sai muka biya kudin fansa har kusan miliyan biyu ga kowane mutum da aka sace,” in ji Aisha.

Ta kara da cewa barayin sun kone rabin kauyen Madira, sun kashe kawunta da ’yan uwansa har guda hudu a gaban jama’a, sun yi garkuwa da mutane sama da 20. Duk da gwamnatin jiha ba ta amince ba, sai suka yi sulhu da barayin.

Aisha ta ce duk lokacin da mutanen Nkaba suka hadu da ’yan Madira sai sun kashe su, suna zarginsu da yin sulhu da ’yan bindiga. A harin da aka kai kwanan nan, sun kashe mutum daya tare da jikkata wani da ke kwance a asibiti.

Ta kuma koka kan yadda rundunar ’yan sanda ta Kaura Namoda ta gaza daukar mataki duk da koken da suka shigar. Ta yi kira ga Gwamnatin Tarayya da Gwamnan Zamfara, Dauda Lawal, da su shiga tsakani domin samar da zaman lafiya tsakanin kauyukan.

Aisha ta ce matsalar ta kara kamari, inda aka samu kashe-kashe da dama, ciki har da wata mata ’yar Madira da ta kai ziyara kauyen Nkaba, da wani mai biredi da aka dauka dan Madira ne, da kuma wani mai achaba da aka sassare.

> “Dole ne mu yi sulhu da ’yan bindiga domin sun hana mu noma, sun hana mu kiwo, sun talauta mu. Barayin suna kawo hari babu kakkautawa, mata, maza, tsofaffi da yara suna gudu, wasu suna fadawa gulbi don tsira. Sun dauki budurwa da karfi, mun sha wahala fiye da shekaru goma,” in ji Aisha.

Ta ce sulhun da suka yi da barayin ya ba su saukin rayuwa, sai dai yanzu mutanen Nkaba suna matsa musu lamba saboda hanyar kauyen Nkaba ce kadai ke kai su shelkwatar Kaura Namoda.

Shugaban Karamar Hukumar Kaura Namoda, Hon. Mannir Haidara, ya tabbatar da samun labarin rikicin, inda ya ce sun tuntubi masarautar Kaura Namoda domin sasanta kauyukan. Ya bayyana cewa an kafa kwamiti domin gudanar da bincike da hukunta duk wanda aka samu da laifi.

> “Ya zama wajibi kauyukan su zauna lafiya da juna. Dukansu musulmai ne, kuma addini ya koyar da kiyaye hakkin ’yan uwantaka. Idan muka gano akwai daukar doka a hannu, za mu hukunta duk wanda aka samu da laifi,” in ji Haidara.

Sai dai duk kokarin jin ta bakin rundunar ’yan sanda da kuma mutanen Nkaba ya ci tura, domin jami’in hulda da jama’a na rundunar ’yan sandan Zamfara, DSP Yazid Abubakar, bai amsa kira ba, haka kuma mutanen Nkaba sun ki cewa uffan game da rikicin.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *