Zan Hada Hannu Da Gwamnati Wajen Bunkasa Yanki Na —Sarkin Tilden Fulani
[ad_1]
Kwanakin da suka gabata ne mai martaba Lamidon Toro na farko Alhaji Umaru Adamu, ya yi bikin nadin Hakimai Biyar da suke a karkashin masarautarsa, wanda Sarkin Garin Tilden Fulani Alhaji Aliyu Muhammadu Tukur na daya daga cikinsu, Wakilinmu na Jos Lawal Umar ya samu ganawa da shi, ga dai yadda hirar ta su ta kasance.
Zan yi farin ciki, idan ka gabatar ma ni da kanka?
Sunana, Alhaji Aliyu Muhammad Tukur, Sarkin Yamman Toro, Hakimin Kasar Tilden Fulani.
Kana daya daga cikin hakimai Biyar, da Mai martaba, Lamidon Toro na daya (1), Alhaji Umar Adamu, ya rantsar a kwanakin da suka gabata don yin aiki tare da shi a fadarsa, ya kaji me kuma za kace?
Naji dadi, koda yake, an kara, daure ni da Sarka ne, don haka dole ne in tashi in yi tsayuwar daka wajen yin aiki tukuru in kuma yi adalci daidai gwargwado, don in sauke nauyin da aka dora mani, don in samu kubuta ranar gobe kiyama. Idan na yi gaskiya shi ne hakan zai bani tsira da ga wadansu tambayoyi da za ayi mani a kabari, ina addu’a Allah S W T ya taimaka mani mini in sauke wannan nauyi da aka dora mani cikin nasara.
Ga shi ka gaji matsaloli masu yawa kama dada wadda ta shafi rashin tsaro, da kuma rashin abubuwan da za su inganta rayuwar al’umma, kamar rashin ingantccen ruwan sha, ta yaya za ka iya fuskantar lamarin?
Zan fara da matsalar rashin tsaro, domin ita ce tafi tayar da hankalin jama’a, ba nan yanki na kawai ba, Kusan dukkan kasa baki daya, maganar rashin tsaro ita ce tafi tayarwa mutane hankali, zan kara yin kokari in ga ‘yan bangarmu sun kara hada kai da jami’an tsaro da suka hada da sojoji, da ‘yansanda da aka turo su aiki, a nan yankin domin su rika aiki tare dare da rana, wajen yin yaki da miyagun mutane masu kawo barazana da rayuwar al’umma.
Zan kuma bukaci babban jami’in ‘yansanda, (DPO) na wannan gari da shugabannin addini da na al’ummomi, da na ‘yansiyasa, da sauran kungiyoyi, da ke zaune, a wannan yanki da su kara badai hadin kai wajen cimma wannan burin. Za kuma mu toshe duk wata kofa da muke ganin mugayen mutane za su iya yin amfani da ita domin su aikata barna, masu unguwanni kuma su tabbatar da sun tantance bako kafin su bari ya sayi gida ko Folotin, da zai gina gida ko kuma gonar da zai yi noma.
Duk da yake a baya an taba baka wannan mukami amma daga baya aka soke sai kuma ga shi wannan gwamwnatin karkashin jagorancin Gwamnan Jihar Bauchi Sanata Bala Mohammed, ya sake maida maka da mukamin ya kaji maye za kace?
Na ji dadi ba abinda zan ce sai dai, in kara yi wa Allah godiya da ya kawo mu zuwa wannan lokaci ga gwamnan mu Sanata Bala Mohammed ina mai godiya kwarai da gaske, domin da a baya tsohon Gwamna Isa Yuguda, ya nada mu wadannan mukamai na Hakimai, amma daga baya Gwamnan Muhammed Abubakar, ya zo ya sauke mu, ga shi yanzu wannan gwamna mai adalci, ya sake maido mana da mukaman har ma ya kara kirkiro da sabbin masarautu da kuma daga darajar wadansu, ba abinda za nce wa gwamna sai dai in kara yin masa addu’a, Allah ya kara taimaka masa akan kokarin da yake na kawo ci gaban al’umna da na tattalin arzikin jiha, ya kuma kara ba shi lafiya da basiràr ta tafiyar da ayyukan sa cikin nasara.
Ka san cewa zaka yi aiki tare da maimartaba Lamidon Toro,na farko Alhaji Umar Adamu, wane tabbaci za ka yi masa na samun goyon bayan al’ummar masarautarka?
Mai Martaba Lamidon Toro, Alhaji Umar Adamu, ina kara tabbatar masa samun goyon mutanen wannan gunduma dari bisa dari, akan duk wani aiki da zai iya tasowa don ci gaban mutanen wannan karamar hukuma da kuma jihar Bauchi baki daya.
Kasancewa kasar ka ta yi iyaka da jihar Filato, da rikice- rikicen siyasa da na kabilanci, yaki ci yaki cinyewa wane kokari za ka yi wajen kawo hadin kai a tsakanin al’ummomin da ke zaune nan yankin kasar ka da na jihar Filato?
Wannan na daya daga cikin abinda ya fi damuna, domin wannan rikici ya dauki lokaci mai tsawo tun a shekarar 2001, da aka fara rikici a tsakanin al’ummomin jihar Filato, da da su ke zaune lami lafiya da junansu amma ga shi har yanzu ba’ a daina fada ba, ga shi har an kai shekara Ashirin da biyar ke nan wannan ai abin damuwa ne matuka, ina fata gwamnati da masu ruwa da tsaki akan harkar kawo zaman lafiya a Filato za su dauki sabbin matakai don kawo karshen wannan rikicin.
Ya ce, rikicin ya haddasa kwararowar baki masu dimbin yawa zuwa yankin gundumar sa kuma ya bukaci gwamnatin jihar Bauchi da gwamnatin tarayya, da su taimakawa al’ummomin da su ke zaune, a yankin da abubuwan more rayuwar jama’a.
Bugu da kari saboda karuwar al’umma mutanen yankin na fuskantar karancin ababen more rayuwa kamar tsaftatatcen ruwan sha, rashin ingantancen hasken-wutar lantarki, rashin ingantattun hanyoyin-mota daga karkara zuwa birane, karancin azuzuwa na makarantun gwamnati, da kuma karancin jami’an tsaro da dai sauransu.
Kungiyoyin al’umma da na addinai, da na yan-siyasa, da mutane sai zuwa suke yi Fadar Sarkin suke yi don nuna mubaya’arsu da taya shi murna da addu’o’in fatan alkhairi su ke ta yi.
Baki mai kyau
Nima na gode
[ad_2]
Source link