Amotekun Ta Kuɓutar Da Ma’aikatan Lafiya 3 Da Wasu Biyu Daga Hannun Masu Satar Mutane

[ad_1]

Hukumar tsaro ta yankin Arewa maso Yamma Amotekun, reshen jihar Ondo ta kuɓutar da mutum biyar daga masu garkuwa da mutane a yayin wani sumamen cikin dare a Akure ta kudu.

Rahotanni sun ce an sace ma’aikatan lafiya uku a cibiyar Oke-Ijebu da misalin ƙarfe 2 na dare, bayan da maharan suka kutsa cikin wurin ta ƙarfin tsiya suka tafi da su.

  • Hisbah Ta Haramta Gidajen Casun Dare A Katsina
  • An Gurfanar Da El-Rufai A Kotun Kaduna, An Hana ‘Yan Jarida Shiga

Kwamandan Amotekun, Adetunji Adeleye, ya tabbatar da nasarar aikin a Akure. Ya ce an kuɓutar da mutanen bayan artabu mai zafi da masu garkuwar.

Haka kuma an ceto wani mutum mai shekara 45 da ɗansa mai shekara 15 a wani lamari daban. An same su a hanyar Oda Akure bayan harin da aka kai musu da yamma.

Adeleye ya jaddada cewa ana kula da waɗanda aka ceto a cibiyar lafiya ta Amotekun. Ya kuma buƙaci jama’a su ci gaba da bai wa jami’an tsaro bayanai kan lokaci.

Gwamnatin jihar ta tabbatar da cewa tsaron rayuka da dukiyoyi ne ke kan a gaba a wurinta. Ta kuma jaddada muhimmancin haɗin kan jama’a wajen yaƙi da masu aikata laifi.

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *