Hanyoyin Inganta Lafiyar Kwakwalwa
[ad_1]
Akwai dabaru da dama wajen inganta lafiyar kwakwalwa da suka hada da motsa jiki akai-akai da yin wasanni da dai sauran su.
A yau, za mu bayar da shawarwarin inganta lafiyar kwakwalwa wadada idan ana aiwatarwa da su za su taimaka wa jin dadin rayuwa.
Hulda Da Sauran Mutane
Halda da abokai da dangi akai-akai yana da muhimmanci ga jin dadin zuciya da lafiyar jiki gaba daya. Bincike ya nuna cewa zaman kadaici yana da tasiri sosai wajen haifar da damuwa da tashin hankali.
Don haka, yi kokari ka dunga hulda da mutane akai-akai da tsara lokutan haduwa, kuma ka dunga fita waje don gudanar da abubuwa na zamantakewa. Za ka ji dadi sosai.
Saboda haka, yana da muhimmanci ka inganta lafiyarka kuma ka san iyakokinka. Ka da ka zama mutum mara yin mu’amala, domin za rasa abubuwa masu yawa. Ka koyi abubuwan da ya kamata ka yi da wadanda ba su kamata ba.
Kasance Da Tsarin Kula Da Kanka A Kullum
Mutane da yawa sun kasance suna ciki aiki a ko da yaushe, karatu da kula da iyali da gida har suna manta da kula da kansu. Amma, kamar yadda injin ke bukatar kulawa akai-akai don ya yi aiki cikin sauki, haka muke bukata.
Kuma yayin da injin zai iya bukatar canjin mai, muna bukatar tsarin kula da kai wanda ya hada da abubuwan da suke amfani a gare mu don mu ji dadi. Wannan na iya hadawa da abubuwa iri-iri, amma galibi yana ta’allaka ne a kan: motsa jiki akai-akai da aiki a kullum da koyo da kokarin tsarkake zuciyarka na ‘yan mintuna da rubuta abubuwa ta amfani da alkalami da takarda, misali, rubuta abubuwan da kake godiya da su.
Karatu cikin nishadi ko don koyon abubuwa sabbi da barin kallon ‘screen’ na wani lokaci da barin waya a gida domin zuciyarka ta huta.
Don haka, za ka iya kara wasu abubuwan da za su taimaka maka. Misali, man shafawa na iya inganta lafiya. An nuna cewa yana inganta nutsuwa da kuma inganta barci.
Bayar Da Muhimmanci Ga Barci
Akwai alaka mai karfi tsakanin barci da lafiyar kwakwalwa. Alal asali, barci yana ba mu damar yin aiki cikin inganci, jin dadin kanmu, da kuma tunani da kyau, duk suna da muhimmanci ga lafiya.
Bincike ya gano alaka mai karfi tsakanin rashin barci da karin hadarin samun matsalolin kwakwalwa, ciki har da damuwa, fushi, rashin iya sarrafa dabi’a, da sauran matsaloli.
Ga wasu hanyoyi masu da za a iya inganta barci da suka hada da:
Kwaciya a kan gado da wuri da tashi da wuri da motsa jiki a kullum (amma ka da a yi mai yawa a lokacin bacci) da guji shan giya da yamma da shan kofi awanni 8 kafin lokacin kwanciya da kashe wuta a dare, karantu, yin tunani, wanka, da sauransu.
Yin Aiki Kan Wani Abu Da Kake Jin Dadi
Wasu bincike sun nuna cewa samun lokaci don ayyukan nishadi yana da nasaba da inganta lafiyar kwakwalwa, hangen nesa, da kwanciyar hankali. Wasanni su ne suka fi dace da wannan rukunin, saboda suna iya zama nishadi, taimaka maka samun sauki, da cire hankalinka daga wasu abubuwa.
Don haka, ko kana son kamun kifi, yin wasa, tattara abubuwa, ko yin wani abu na daban, samun lokaci don yin atisaye zai iya kawo babban bambanci.
Kula Da Daidaita Aiki Da Rayuwa
Daidaita aikin da rayuwa na iya zama abu mai kyau idan kuna son samun nutsuwa. Aiki yana da muhimmanci, amma zai iya haifar da lahani fiye da amfaninsa idan kuka bari ya mamaye dukkan rayuwarku.
Ga wasu shawarwari don inganta daidaiton aiki da rayuwa wadanda suka hada da:
Samun lokutan aiki da kuma tsayayuwa a kansu, ka da ka amsa kiran waya, sakonni a yayin lokacin hutunka, ka koyi yadda ake fadin “a’a” ga karin ayyuka, musamman wadanda ba za a biya ka ba, sannan ka yi hutu a wurin aiki ko hutu na minti 5 na iya tsaftace zuciyarka da inganta lafiyar kwakwalwarka.
Kammalawa
Tambaya, “Ta yaya za a inganta lafiyar kwakwalwa?” tana da amsoshi da dama. Wasu dabaru na iya yin aiki mafi kyau a gare ka fiye da wasu, don haka yana da kyau a gwada su don ganin wanne ya fi dacewa.
[ad_2]
Source link