2027: Ministocin Da Ake Tsammanin Za Su Yi Murabus Kafin Wa’adin Tinubu Na Ranar 31 ga Maris
[ad_1]
Akalla ministoci shida a cikin majalisar zartarwar Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu na iya yin murabus kafin cikar wa’adin shugaban kasa na ranar 31 ga Maris ga masu mukaman siyasa da ke neman tsayawa takara a zaben 2027.
Wani umarni daga Tinubu, wanda ofishin sakataren gwamnatin tarayya, George Akume, ya bayar, ya umarci duk jami’an da abin ya shafa su yi murabus kafin shiga zabukan fid da gwani na jam’iyyu.
An bayar da umarni ne bisa sashe na 88(1) na dokar zabe ta 2026, da kuma jadawalin da hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) ta fitar kan zaben fitar da gwani na jam’iyyun siyasa kafin zaben 2027.
A cikin wata sanarwa da Akume ya sanya hannu kuma aka fitar daga hannun babban sakataren ofishin, Ibrahim Abubakar Kana, gwamnati ta bayyana cewa na bukatar yin murabus na dukkan masu rike da mukaman siyasa da shugaban kasa ya nada, ciki har da ministoci, masu ba da shawara na musamman, manyan mataimakan na musamman, da shugabannin hukumomin tarayya.
“Dukkan jami’an da abin ya shafa ana bukatar su mika wasikun murabus dinsu ta ofishin sakataren gwamnatin tarayya ba tare da wuce ranar 31 ga Maris, 2026 ba,” in ji sanarwar.
Kafin wa’adin ya cika, rahotani sun yi tsammai wasu ministoci wadanda ka iya bin umarnin domin shiga cikin tsarin samun tikitin gwamna a jam’iyyar APC a jihohinsu. Wasu daga cikin ministocin kamar haka:
Ministan Wutar Lantarki, Bayo Adelabu
Bayo Adelabu na cikin manyan shahararrun mutane da za su iya barin majalisar zartaswar Tinubu. Ya kasance tsohon mataimakin gwamnan Babban Bankin Nijeriya (CBN), ya gina kyakkyawan matsayin siyasa a Jihar Oyo a cikin shekaru goma da suka gabata.
Adelabu ya tsaya takarar gwamnan jihar a shekarar 2019 karkashin jam’iyyar APC, sannan kuma a shekarar 2023, ya tsaya a karkashin Jam’iyyar Accord, inda ya sha kaye duka a hannun Gwamna Seyi Makinde. Burinsa na sake neman takara a 2027 ana ganin shi a matsayin ci gaba da dogon aikin siyasa da yake da shi a jihar.
An ruwaito cewa Adelabu ya bayyana a niyarsa a watan Oktoba 2025, cewa shi ne zai zama gwamnan Jihar Oyo a 2027.
A cikin wani bidiyo da Adelabu ke yin jawabi a wani taro, ya ce burinsa ba saboda son kai ba ne amma saboda ainihin sha’awar inganta rayuwar mutanen Jihar Oyo ne.
Ministan Lafiya Da Walwalar Jama‘a,
Ministan lafiya da walwalar jama’a, Muhammad Ali Pate, kwararren masani ne a fannin kiwon lafiya wanda ya samu kwarewa a matakin kasa da kasa. A baya ya yi aiki a matsayin karamin ministan lafiya a tsakanin watan Yulin 2011 zuwa Yuli 2013 a karkashin tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan, sannan daga baya ya yi aiki a matsayin daraktan cibiyar kudi ta Dduniya (GFF) da ke karkashin Bankin Duniya.
Pate ya taba tsayawa takarar gwamnan Gombe a baya kuma har yanzu yana da tasiri a siyasar jihar, abin da ke ci gaba da sanya shi cikin jerin masu yiwuwar tsayawa takara a 2027.
An ya ruwaito cewa wasu kungiyoyi sun ci gaba da bayyana shi a matsayin dan takara mai karfi a zaben gwamnan Gombe a shekarar 2027. Daya daga cikin irin wadannan kungiyoyin sun hada da kungiyar tsofaffin daliban makarantar firamare ta Bakaro/Dangikka, ta bayyana shi a matsayin dan takarar da ya dace da wannan mukami.
A cikin wata sanarwa da sakataren janar na kungiyar, Umar Musa, ya sanya hannu, mai taken “Dalilin da ya sa Gombe ke bukatar Farfesa Ali Pate a matsayin gwamna a 2027”, kungiyar ta bukaci shi ya yi takara, inda ta bayyana cewa, “Lokaci ya yi na sabon zamani na shugabanci mai ma’ana da ci gaba a Jihar Bauchi tare da hangen nesa, kwarewa da sadaukarwa ga hidimin jama’a.
“A ra’ayinmu ministan harkokin lafiya da walwalar jama’a, Farfesa Mohammed Ali Pate shi ne mutumin da ya fi dacewa da kujerar gwamnan Gombe a 2027.
“Pate shi ne ministan harkokin lafiya da walwalar jama’a. Nasarori da cancantarsa su ne suka sanya shi ya zama dan takara mafi dacewa, wanda yake da duk abin da ake bukata don zama gwamnan Jihar Gombe a 2027.”
Ministan Noma Da Samar Da Abinci, Abubakar Kyari
An fara zaben Kyari zuwa majalisar wakilai a shekarar 1998 a lokacin mulkin soja na Janar Sani Abacha karkashin tutar jam’iyyar UNCP. Daga baya ya koma jam’iyyar APC, ya yi aiki a matsayin mataimakin shugaban jam’iyyar na arewa, matsayin da ya karfafa tasirinsa a cikin jam’iyyar.
An zabe shi zuwa majalisar dattawa a shekarar 2015 karkashin tutar jam’iyyar APC kuma an sake zabe shi a shekarar 2019, ya yi aiki har zuwa Afrilun 2022 lokacin da ya yi murabus domin daukar matsayin mataimakin shugaban jam’iyyar na arewa. Ya yi dan gajeren lokaci yana aiki a matsayin mukaddashin shugaban jam’iyyar a watan Yulin 2023 bayan murabus din Abdullahi Adamu, kafin a nadinshi a matsayin ministan noma da samar da abinci ta cikin majalisar zartarwar Shugaba kasa Bola Tinubu a watan Agusta 2023 bayan amincewar majalisar dattawa.
Ko da yake bai yi wata sanarwa a hukumace ba, amma kungiyoyi da dama, ciki har da Borno ‘Social Media Frontiers’ (BSF), sun nuna Kyari a matsayin dan takara gwamnan Jihar Borno da zai gaji Babagana Umara Zulum.
Ministan Sufuri, Saidu Alkali
Tsohon sanatan da ya yi wa’adi har guda uku wanda ya wakilci Gombe ta arewa a majalisu na 6, 7 da na 9, ana ganin yana aiki daga Abuja don samun tikitin gwamna na APC a Jihar Gombe.
Kwarewar siyasar Alkali ya shafi rawar da ya taka a majalisar dokoki da na zartarwa. A baya ya yi aiki a matsayin kwamishina yada labarai a Jihar Gombe, sannan daga baya ya shugabanci kwamitin majalisar dattawa kan harkokin sojan saman Nijeriya.
Kwarewarsa da hanyar sadarwarsa na siyasa sun sa da yawa suna hasashen zai iya samun tikitin takarar gwamnan APC a jihar.
Ministan Harkokin Waje, Yusuf Maitama Tuggar
Ana sa ran Yusuf Maitama Tuggar zai bar majalisar ministoci don cimma burinsa na zama gwamnan Jihar Bauchi, wanda zai shiga cikin wadanda za su fafatawa takara a cikin jam’iyyar APC.
A baya ya yi aiki a matsayin mamba na majalisar wakilai daga 2007 zuwa 2011, ya wakilci mazabar Gamawa, kuma ya yi takarar gwamnan sau biyu.
Burinsa ya fara tun daga shekara ta 2011 lokacin da ya tsaya takara karkashin jam’iyyar CPC, sannan kuma a shekara ta 2015 lokacin da ya sha kaye a zabukan fid da gwani na APC. A yanzu ana ganin shi a matsayin dan takara mai karfi wajen fafatawa a jihar.
Wata kungiyar masu matsin lamba da ke Bauchi, ta yi kira ga Tuggar a wani taro da aka gudanar ‘yan watanni da suka gabata da ya shiga takarar zaben gwamna na 2027, tana mai jaddada bukatar mulkin jiyar ya juya zuwa Bauchi ta arewa bayan shekaru na shugabancin Bauchi ta kudu.
Wani dattijo na APC, Abdullahi Usman Matori, wanda ya yi magana a taron, ya kare kiran da ake yi na cewa Bauchi ta arewa su samar da gwamnan jihar na gaba, yana mai lura cewa Bauchi ta kudu ta rike wannan matsayi tun daga 1999.
Ministan Sadarwa Da Tattalin Arzikin Zamani, Bosun Tijani
Bosun Tijani, ana yawan girmama shi saboda kwarewarsa a fannin fasaha. Yana daya daga cikin wadanda suka kafa ‘Co-Creation Hub’ (CcHUB), daya daga cikin manyan cibiyoyin kirkira a Afirka, kuma ya samu digirin digirgir a fannin kirƙira da ci gaban tattalin arziki daga Jami’ar Leicester a 2023.
Tun lokacin da aka nada shi, ya mai da hankali kan kayayyakin more rayuwa na zamani da tallafa wa ci gaban tattalin arziki da fasaha ke jagoranta.
Ko da yake bai bayyana niyyarsa ta tsayawa takarar gwamna tun da dadewa, an kuma ambaci Tijani a matsayin mai yiwuwa ya tsaya takarar gwamnan Jihar Ogun a 2027.
[ad_2]
Source link