Atiku Ne Ya Fi Dacewa Da Tikitin Takara A ADC Amma Ya Kamata Ya Janye — Baba-Ahmed
Tsohon Mai Bai wa Shugaban Ƙasa Shawara kan Harkokin Siyasa a Ofishin Mataimakin Shugaban Ƙasa, Dr. Hakeem Baba-Ahmed, ya ce duk da cewa tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa Atiku Abubakar, shi ne ya fi cancanta ya samu tikitin shugaban ƙasa na jam’iyyar ADC, gudummawar da ta fi dacewa da zai bai wa Nijeriya ita ce ya janye daga takarar zaɓen 2027.
Baba-Ahmed ya bayyana haka ne yayin da yake jawabi a shirin tashar talabijin na Arise News, a safiyar ranar Alhamis, inda ya ce janyewar Atiku daga takarar za ta aika da saƙo mai ƙarfi kan sabon tsarin siyasa da kuma kawo ƙarshen ci gaba da sake jujjuya tsofaffin ’yan siyasa.
- AFCON 2025: CAF Ta Ci Tarar Algeria, Ta Dakatar Da Ƴan Wasanta
- Kotun Koli Ta Yi Watsi Da Ƙarar Kisan Kudirat Abiola, Ta Sallami Al-Mustapha
A cewarsa matakin da Atiku zai ɗauka na haƙura da tsayawa takara “babbar shawara ce da ta kamata ya yi tunani a kai” wadda za ta iya sauya yanayin siyasar adawa tare da ƙarfafa sauyin zamani kafin zaɓen 2027.
Duk da amincewa da ƙwarewar Atiku a siyasa da kuma tasirinsa, Baba-Ahmed ya ce tsohon mataimakin shugaban ƙasar har yanzu shi ne kan gaba a jam’iyyar ADC, duba da yadda ya shahara a ƙasa baki ɗaya, da muhimman tsare-tsare da kuma amincewar da mabiyansa suka da shi.
Sai dai Baba-Ahmed, wanda tsohon kakakin Ƙungiyar Dattawan Arewa (NEF), ya soki ra’ayin ware tikitin ADC ga mutum ɗaya, yana mai gargaɗin cewa hakan ya saɓa wa ƙa’idojin dimokuraɗiyya.
Duk da amincewarsa da fifikon da Atiku ke da shi kan sauran masu neman takarar shugaban ƙasa, Baba-Ahmed ya jaddada cewa ya dace tsohon mataimakin shugaban ƙasar ya yi la’akari da janyewa domin ci gaban ƙasa baki ɗaya.