Bunkasar Tattalin Arzikin Sin: Ya Kamata Afirka Ta Dama Idan Dama Ta Samu

[ad_1]

Bunkasar tattalin arzikin kasar Sin da kashi 5 cikin dari a shekarar 2025 cikin yanayi mai sarkakiya na kasa da kasa, wanda ya kunshi sauye‑sauyen kasuwanci, hauhawar farashi a duniya, kalubalen basussuka, da rikice‑rikicen tattalin arziki tsakanin manyan kasashe, wata dama ce ga kasashen Afirka da ta kamata su dama a ciki ba tare da sanya ba.

Sakamakon yanayi mai rikitarwa da duniya ke kara-kaina a ciki, ci gaban tattalin arzikin Sin ya zama wani ginshiki na samar da kwanciyar hankali a bangaren kasuwancin duniya musamman ma yadda ya ci gaba da ba da gudunmawar kashi 30 cikin dari na jimillar tattalin arzikin duniya baki daya. Afirka, wadda ke da alaka mai zurfi da kasar Sin ta fuskar kasuwanci da zuba jari, na iya kara cin gajiyar hakan ta hanyar albarkatun kasa, musamman ma’adanai, makamashi, da kayayyakin noma, ko da kuwa kasuwannin wasu abokan huldarsu sun yi tutsu.

Matukar an samar da tsayayyun manufofi da yanayi mai dacewa da zuba jari, wannan zai kara bai wa Afirka damar jawo zuba jari kai-tsaye daga kasar Sin, musamman a fannonin da aka rika aka kulla kawance kamar ababen more rayuwa, masana’antu, makamashi, fasahar zamani da sauransu.

Kazalika, sauye‑sauyen da kasar Sin take ta yekuwar tabbatarwa a tsarin tafiyar da tattalin arzikin duniya domin karfafa kasashe masu tasowa da kokarin rage dogaro da wuri guda wajen samar da kayayyaki, na kara bude wa Afirka kofa wajen shiga tsarin samar da kayayyaki na duniya, ta yadda nahiyar za ta samu damar fitar da kayayyakin da ta sarrafa maimakon dogaro da cinikin danyen albarkatun kasa kawai.

Sai dai kuma, domin kar wannan dama ta zama “ga koshi ga kwanan yunwa”, wajibi ne gwamnatocin Afirka su kara yin hobbasa a bangaren tsara muradun tattalin arziki na dogon zango, da dabarun fuskantar kalubalen da za su biyo baya musamman daga sauran kasuwannin duniya da kuma sauyin yanayi. Mun riga mun ga makirce-makircen da ake ta kulla wa manyan kasashen nahiyar bisa farkawarsu da kuma alakar da suke zurfafawa da Sin a matsayin aminiyarsu. Ana ta kokarin mayar da hannun agogo baya ta hanyar rura wutar rikicin addini da kabilanci, har ma da na bangaranci.

A takaice dai, a cikin wannan yanayi mai sarkakiya na kasa da kasa, ci gaban da tattalin arzikin kasar Sin ya samu na kashi 5 cikin dari a 2025 wani ginshiki ne da Afirka za ta iya dogaro da shi, saboda Sin ita ce babbar abokiyar cinikin nahiyar har na tsawon kimanin shekaru 16 a jere, sannan ga manufar soke haraji ga kayayyakin galibin kasashen nahiyar masu huldar diflomasiyya da ita da ake kawowa kasuwarta. Amma kuma nasarar hakan za ta rataya ce kan iya daidaita damammakin da kuma kalubale cikin tsari, hangen nesa, da ingantaccen tsarin shugabanci na-gari. (Abdulrazaq Yahuza Jere)

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *