Gobara ta ƙone shaguna 22 a kasuwar shanu a Kwara

[ad_1]



Aƙalla shaguna 22 ne suka ƙone ƙurmus sakamakon gobara da ta tashi a Kasuwar Kara ta Ajase-Ipo, da ke Ƙaramar Hukumar Irepodun, a Jihar Kwara.

Gobara ta tashi ne da misalin ƙarfe 1:35 na daren ranar Laraba, bayan wutar girki da ba a kashe ta da kyau ba ta tashi a ɗaya daga cikin shagunan katako.

Daga baya wutar ta bazu zuwa sauran shagunan da ke kasuwar.

Ba a tantance adadin kayayyakin da suka ƙone ba, amma ’yan kasuwa sun ce sun tafka asara ta miliyoyin Naira.

Mai magana da yawun Hukumar Kashe Gobara ta Jihar Kwara, Hassan Hakeem Adekunle, ya ce jami’ansu sun samu damar dakatar da wutar kafin ta kai ga inda ake ɗaure dabbobi.

Ya bayyana cewa daga cikin shaguna 323 da ke kasuwar, gobarar ta ƙone shagunan katako 22 da kuma shagunan kwantena guda shida.

Shagunan da abin ya shafa, ana sayar da kayan abinci kamar shinkafa, garin doya, masara, gero da dawa, yayin da kwantenan suka ƙunshi kayan masarufi da abubuwan amfani na yau da kullum.

Jami’an kashe gobara sun shafe tsawon dare suna aiki don hana wutar ƙara bazuwa.

Daraktan hukumar ya yaba wa jami’an kan yadda suka kai wa ɗaruruwan shaguna da kadarori ɗauki.

Adekunle, ya shawarci ’yan kasuwa da mazauna yankin da su riƙa kiyaye hanyoyin kare tashin gobara tare da guje wa sakaci, musamman a kasuwanni da ake da kayayyakin da ke iya kamawa da wuta cikin sauƙi.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *