Kasashen Sin Da Amurka Na Tuntubar Juna Dangane Da Ziyarar Shugaba Trump
[ad_1]
Ma’aikatar harkokin wajen Sin ta ce kasashen Sin da Amurka na tuntubar juna dangane da ziyarar da shugaban Amurka Donald Trump zai kawo kasar Sin.
Kakakin ma’aikatar Lin Jian ne ya bayyana haka yayin taron manema labarai na yau Litinin, a lokacin da yake amsa tambayar da aka yi masa game da batun, inda ya ce hulda tsakanin shugabannin kasashen biyu na da matukar muhimmanci wajen jangorantar dangantakar kasashensu.
Da aka nemi jin ta bakinsa game da furucin shugaban Amurka kan kasar Sin, game da mashingin Hormuz, Lin Jian ya ce karuwar tashin hankali a mashigin da kewayensa, ya katse hanyoyin jigilar kayayyaki da na cinikin makamashi na kasa da kasa, tare da kawo tsaiko ga zaman lafiya a yankin da ma duniya.
Kakakin ya kuma yi kira ga dukkan bangarorin da su dakatar da aiwatar da matakan soji nan take, su kaucewa kara ta’azzara rikicin, da kare tashin hankali a yankin daga yin mummunan tasiri ga ci gaban tattalin arzikin duniya. (FMM)
[ad_2]
Source link