An naɗa Remi Tinubu Sarauniyar Yaƙin Akko

[ad_1]



Lamidon Akko da ke jihar Gombe, Alhaji Umar Muhammad Atiku, ya nada Uwargidan Shugaban Najeriya Sanata Remi Tinubu, sarautar Sarauniyar Yaki a masarautar.

Basaraken dai ya karrama uwargidan shugaban ƙasar ce a ranar Alhamis a wani biki na musamman da ya gudana a fadarsa.

A cewar basaraken, ya ba ta sarautar ce domin yabawa da gudummawar da take bayarwa wajen kare marasa ƙarfi tare da tallafawa mata da yara a fadin ƙasar nan

A yayin ziyarar kwanaki biyu da ta kai jihar Gombe, Remi Tinubu ta kuma ƙaddamar da shirin Renewed Hope Initiative Flow With Confidence, wani muhimmin shiri na tsaftar al’ada, wanda zai samar da kayan tsaftar jinin al’ada ga ‘yan mata a makarantu, domin rage yawan rasa darussa da suke yi a lokacin al’ada.

Bayan an nada ta a sarautar, Sanata Remi ta bayyana farin cikinta da godiya, tana mai cewa wannan karramawa abar girmamawa ce da kuma ƙarfafa gwiwa a gare ta.

Ta yi alkawarin ƙara yin himma wajen tallafa wa ‘ya‘ya mata musamman a fannonin ilimi da lafiya, tare da roƙon sarakunan gargajiya da su taimaka wajen yada shirye-shiryenta har zuwa yankunansu.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *