Kotu Ta Amince Da Aiwatar Da Sabbin Dokokin Haraji Daga 1 Ga Janairu
[ad_1]
Wata Babbar Kotu a Abuja ta ba Gwamnatin Tarayya, Hukumar tattara Haraji ta Cikin Gida (FIRS), da Majalisar Dokoki ta Ƙasa izinin ci gaba da aiwatar da sabon tsarin haraji da aka tsara zai fara aiki a ranar 1 ga Janairu, 2026, bayan ta yi watsi da ƙarar da ke neman dakatar da shirin.
Hukuncin, wanda Mai Shari’a Kawu ya yanke a ranar Talata, ya soke buƙatar da kungiyar ‘Incorporated Trustees of African Initiative for Abuse Public Trustees’ ta shigar, wadda ta nemi umarnin hana gwamnati da hukumomin da abin ya shafa aiwatar da Dokar Harajin Nijeriya, 2025, Dokar Gudanar da Harajin Nijeriya, 2025, da Dokar Hukumar Harajin Nijeriya, 2025.
Masu shigar da ƙara, sun nemi kotun da ta dakatar da aiwatar da sabuwar dokar haraji har sai an fayyace zargin sauye-sauyen da dokar ta ƙunsa da kuma keta wasu tanade-tanaden dokar ƙasa.
Amma duk da haka, Mai Shari’a Kawu ya yanke hukuncin cewa, ƙarar ba ta da inganci kuma ta kasa nuna yadda aiwatar da sabbin dokokin harajin zai haifar da illar da ba za a iya gyarawa ba ko kuma ta karya duk wani tanadin kundin tsarin mulki. Kotun ta jaddada cewa batutuwan da suka shafi manufofin kuɗi da gyare-gyaren tattalin arziki sun rataya ne ƙarƙashin ikon gwamnati kamar yadda doka ta tanada.
[ad_2]
Source link