Yadda Ci Gaban Aikin Noma Na Sin Ke Samar Da Alfanu Ga Afirka

[ad_1]

Kwanan nan, jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin ta gudanar da babban taro kan ayyukan noma, inda aka tsara ayyukan raya ayyukan gona da kauyuka da kuma manoma cikin sabuwar shekara. A matsayinta na babbar kasa mai yawan mutane kimanin biliyan 1.4, gudanar da ayyukan noma da bunkasa ci gaban kauyuka da manoma daidai yadda ya kamata, da kuma samar da isashen abinci bisa karfin kanta, tushe ne na bunkasar kasar ta Sin, wanda hakan ke da matukar ma’ana wajen zamanantar da kasar.

Daga fuskantar talauci da rashin wadataccen abinci, zuwa samun isasshen abinci da kuma saurin ci gaban fasahar noma, Sin ba wai kawai ta dogara da kanta wajen biya bukatun jama’arta ta fannin abinci ba, har ma ta raba nasarorinta ga kasashe masu tasowa da ke ci gaba da fuskantar matsalolin rashin isashen abinci, musamman ma kasashen Afirka.

A cikin ‘yan shekarun nan, Sin da kasashen Afirka sun sami nasarori masu kyau bisa hadin gwiwarsu ta fannin aikin noma, har ma yawan cibiyoyin gwada fasahohin noma da Sin ta kafa a kasashen Afirka sun kai sama da 20, matakin da ya horar da dubban ma’aikatan fasahohin noma a wuraren.

A kasashe kamar Burundi da Madagascar, shinkafar da aka inganta irinta da Sin ta kirkiro ta ba su damar girbin shinkafa da yawansa ya ninka sau 2 ko 3 bisa na lokacin da. A Rwanda da Mauritania, ana amfani da fasahar Juncao ta kasar Sin, wajen samar da harawa da noman laimar kwado, da kuma hana kwararowar hamada. A Kwadibuwa, tsarin sarrafa shinkafar da Sin ta bayar ya inganta wannan aiki bisa karuwar kashi 15%. Kuma ana taimaka wa Kenya da Madagascar wajen karfafa ingancin amfanin gona irinsu dangin gyada na Macadamia, da naman rago da sauransu, don su shiga kasuwar Sin.

Gogewa da dabarun ci gaban aikin noma na Sin tana amfanar da kasashen Afirka, kuma an yi imani cewa a nan gaba, kowane mataki na ci gaban aikin noma na Sin ba kawai zai kyauatata zaman rayuwar Sinawa ba, har ma zai taimaka wa kasashen Afirka su cimma burinsu na tsayawa da kafufuwansu wajen samun isasshen abinci, tare da zamanantar da aikin noma a kasashen.(Mai zane da rubutu: MINA)

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *