Yadda Gobara Ta Ƙone Shaguna 25 A Kasuwar Singa A Kano
[ad_1]
Gobara ta tashi da safiyar ranar Litinin a kasuwar Singa da ke Jihar Kano, inda ta lalata shaguna aƙalla 25 kafin jami’an kashe gobara su kashe ta.
Mai magana da yawun Hukumar Kashe Gobara ta Jihar Kano, ACFO Saminu Yusif Abdullahi, ya ce sun samu kiran gaggawa da misalin ƙarfe 5 na safe daga wani mutum mai suna Mubarak Muhammad wanda ya sanar da tashin gobarar.
Jami’an hukumar sun garzaya wajen inda suka tarar da wani bene mai hawa ɗaya, mai ɗauke da Alhaji Abdulmunafi Yunusa, yana ci da wuta.
Wutar ta ƙone shaguna 25 da ke gaban ginin da kuma ɗakunan ajiya kayayyaki 19, amma an samu damar kare ɗakunan ajiya 24 da ke saman bene da kuma duk waɗanda ke ƙasa.
Abdullahi, ya ce tarakta da manyan motoci da aka ajiye a kusa da benen sun hana su isa wajen da wuri.
Rahoton hukumar ya nuna cewa gobarar ta samo asali ne daga matsalar wutar lantarki saboda amfani da wuta ba daidai ba.
Ba a samu asarar rai ba.
Hotuna:
[ad_2]
Source link