Matashi ya kashe abokinsa da wuƙa har lahira a Kano
[ad_1]
Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kano ta tabbatar da cafke wani matashi mai shekara 25, Mustapha Isma’il, bisa zargin caka wa abokinsa, Halifa mai shekara 24, wuƙa.
Matashin ya rasu bayan caka masa wuƙa da Mustapha ya yi sakamakon saɓani da suka samu.
Kakakin rundunar, CSP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya ce lamarin ya faru ne a ranar 26 ga watan Disamba, 2025, da misalin ƙarfe 8:30 na dare, a unguwar Sheshe da ke birnin Kano.
“Bayan samun kiran gaggawa, Kwamishinan ’Yan Sanda, CP Ibrahim Adamu Bakori, ya tura jami’ai zuwa wajen.
“An same wanda aka caka wa wuƙar yana zubar da jini, an garzaya da shi Asibitin Murtala Muhammad, inda likita ya tabbatar da rasuwarsa,” in ji Kiyawa.
Ya ƙara da cewa an kama wanda ake zargin nan take, sannan aka miƙa shi ga Sashen Binciken Manyan Laifuka (CID).
Bincike ya nuna cewa Mustapha ya caka wa mamacin wuƙa a cikinsa bayan wata rigima da ta ɓarke a tsakaninsu.
“Ana ci gaba da bincike, kuma wanda ake zargin ya amsa laifinsa, za a gurfanar da shi gaban kotu bayan kammala bincike.
“Muna kira ga jama’a, musamman matasa, da su kwantar da hankalinsu su guji amfani da makamai duk lokacin da aka samu rashin fahimta,” in ji kakakin ’yan sandan.
Wanda ake zargin ya ce rikicin ya fara ne lokacin da suke kallon fim a waya a gaban wani shago, sai Halifa ya zo da gudu, inda ya gargaɗe shi kada ya lalata masa waya.
Ya ce a lokacin rikicin, mamacin ya doke shi da wani abu, har ya yi masa rauni.
“Na koma gida, na ɗauko wuƙa na caka masa. Daga baya na samu labarin ya rasu.
“Ina nadama da abin da na aikata. Da na san zai rasu, da ban fito daga gida a wannan ranar ba,” in ji shi.
Masu alaƙa
[ad_2]
Source link