NDLEA Ta Kama Mutane 56 A Wuraren Hada-hadar Miyagun Ƙwayoyi A Kano
[ad_1]
Hukumar hana sha da fataucin miyagun ƙwayoyi ta ƙasa, NDLEA, reshen Kano, ta kai samame a wurare da dama da ake sayar da miyagun ƙwayoyi a Jihar Kano, inda ta kama mutane akalla 56, ciki har da wani da ake zargi da hannu a kisan kai da aka yi shekaru biyar da suka gabata.
A cewar hukumar, an samu nasarar kama mutanen ne bayan wani samame na kwanaki uku a jere, wanda aka gudanar mai taken “Operation Ramadan Mubarak” da ake ci gaba da yi.
Jami’in Hulɗa da Jama’a na rundunar, Sadiq Muhammad Maigatari, ne ya tabbatar da kama waɗanda ake zargin a cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Laraba.
Ya ce, “Hukumar NDLEA ta kai samame wurare da dama da ake hada-hadar miyagun ƙwayoyi a faɗin Jihar Kano, tare da kama mutane 56, ciki har da wani da ake zargi da hannu a wani kisan kai da ya faru shekaru biyar da suka gabata, bayan gudanar da aiki na tsawon kwanaki uku a jere a ƙarƙashin shirin ‘Operation Ramadan Mubarak’.”
[ad_2]
Source link