Ban ce Amurka na shirin kawo min hari ba — Sheikh Gumi
[ad_1]
Shahararren malamin addinin Musulunci, Sheikh Ahmad Gumi, ya karyata wani rahoto da ke yawo a kafafen sada zumunta da ke ikirarin cewa ya ce za a kai masa hari daga Amurka a cikin Najeriya, inda ya bayyana labarin a matsayin karya tsagwaronta.
Sheikh Gumi, a shafinsa na Facebook da aka tantance, ya bayyana cewa bai taba fadin hakan ba kuma bai taba tunanin irin wannan abu ba.
“Yanzu haka akwai labarin karya da ke yawo wanda ke ikirarin cewa na ce an kai mini hari daga Amurka a cikin Najeriya, ko makamancin haka,” in ji shi.
Da yake watsi da rahoton, malamin ya kara da cewa: “Ban taba fadin haka ba, kuma ban taba tunanin hakan zai yiwu ba. Ina zaune lafiya a gidana tare da iyalina ba tare da tsoro, barazana, ko fargaba ba.”
Ya bayyana cewa kuskuren fahimtar ya samo asali ne daga wani wa’azi da ya gabatar a masallaci, inda ya bayar da labarin wani tsohon lamari na tsaro da ya shafi Boko Haram.
“Ina ganin tushen wannan kuskuren fahimta shi ne wani wa’azi da na gabatar a masallaci, inda na bayyana yadda a watan Agustan 2012 aka sanar da ni cewa Boko Haram sun yi niyyar kashe ni,” in ji Sheikh Gumi.
A cewarsa, yunkurin ya ci tura ne bayan da maharan suka mutu da bam dinsu. “Mutanen biyu da suka zo aiwatar da shirin sun mutu nan take lokacin da bam din ya tashi a hannunsu kusa da gidana,” in ji shi.
Saboda haka, Sheikh Gumi ya bukaci kafafen yada labarai da suka wallafa rahoton su gyara kuskuren.
“Ina shawartar dukkan gidajen watsa labarai da suka yada wannan labarin karya da su fito fili su janye shi tare da bayar da hakuri,” inji shi.
[ad_2]
Source link