Daga Ƙarshe, Tinubu Ya Naɗa Jakadu Uku Bayan Tsawon Shekara 2 Ana Jira
Shugaba Bola Tinubu ya fara naɗa jakadu uku, wanda hakan ya kawo ƙarshen dogon jiran jerin sunayen jakadu da aka daɗe ana tsumayi tun hawansa karagar mulki.
Waɗanda aka naɗa su ne, Kayode Are daga jihar Ogun, Aminu Dalhatu daga Jigawa da Ayodele Oke daga jihar Oyo.
Shugaban ya aika da jerin sunayen zuwa ga Majalisar Dattawa don tabbatarwa, a ranar Laraba.
“Jerin sunayen ya ƙunshi sunaye uku ne kacal a yanzu, ina da tabbacin wasu za su biyo baya,” in ji Shugaban Majalisar Dattawa Godswill Akpabio bayan karanta wasiƙar Shugaba Bola Tinubu.