ICPC Ta Shirya Gurfanar Da El-Rufai Kan Zargin Cin Hanci A Ranar 24 Ga Maris

[ad_1]

Hukumar ICPC ta sanar da shirinta na gurfanar da Malam Nasir El-Rufai a kotu. Za a gabatar da shi ne a Babbar Kotun Tarayya da ke Kaduna ranar 24 ga Maris, 2026.

A sanarwar da kakakin hukumar, John Odey, ya fitar, an ce zai fuskanci shari’a tare da wani mai suna Joel Adoga. An yi rajistar ƙarar da lamba FHC/KD/73/2026 a sashin shari’a na jihar Kaduna.

  • Bayan Kwana 30, Har Yanzu ICPC Na Ci Gaba Rike El-Rufai
  • El-rufa’i Ba Zai Halarci Taron Jam’iyyar APC Na Kasa Ba, Kuma Ganduje Na Nan A Shugabanci

ICPC ta bayyana cewa tuhumar ta haɗa da karkatar da kadarorin gwamnati da kuma sama da faɗi da kuɗaɗe. Ta jaddada cewa an riga an miƙa masa takardar gayyata kamar yadda doka ta tanada.

Haka kuma an shigar da wata ƙara dabam a Babbar Kotun Jihar Kaduna da lambarr fayal KDH/KAD/ICPC/01/26. A wannan shari’ar, ana tuhumar El-Rufai da wani Amadu Sule da laifukan cin hanci da amfani da muƙami ba daidai ba.

Hukumar ta ce an shigar da dukkanin ƙarar ne a ranar 18 ga Maris, 2026. Ta ƙara da cewa za a sanar da ranar gurfanar da shari’ar jihar nan gaba.

ICPC ta tabbatar da cewa za ta bi dukkan matakan doka a shari’ar.

Rahotanni sun nuna cewa an kama El-Rufai a watan Fabrairu kafin daga bisani ICPC ta riƙe shi har zuwa wannan lokaci. Yanzu haka yana tsare yayin da ake jiran fara shari’ar.

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *