An kashe ’yan Najeriya sama da mutum 1000 cikin wata 2 — Obi

[ad_1]



Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar LP a zaɓen 2023, Peter Obi, ya ce an kashe ’yan Najeriya sama da mutum 1,000 m tsakanin watan Janairu da Fabrairun 2026.

Ya kuma ce an sace dubban mutane a wannan lokaci.

Ya bayyana hakan ne a shafinsa na X a ranar Lahadi.

Obi ya ce irin yawan hare-haren da aka fuskanta a Najeriya ya fi na wasu ƙasashen da ke cikin yaƙi a hukumance.

Ya soki shugabannin siyasa, yana cewa sun fi mayar da hankali kan shirye-shiryen zaɓen 2027 maimakon kare rayukan jama’a.

A cewarsa, hare-haren ’yan bindiga da sauran ’yan ta’adda sun shafi jihohi 25, inda aka samu kashe-kashe, satar mutane, da lalata garuruwa.

Ya ƙara da cewa magidanta da dama a jihohin Zamfara, Binuwai, Filato, Ondo da sauransu sun rasa ’yan uwansu, yayin da wasu jama’a suka tsere daga gidajensu saboda fargabar kai musu hari.

Ya buƙaci gwamnati ta fifita rayukan jama’a.

“Abin damuwa ne sosai ganin yadda ’yan siyasa ke ta shirye-shiryen tunkarar zaɓen 2027, alhali an kashe m ’yan Najeriya sama da 1,000, kuma an sace mutane da yawa cikin watanni biyu kacal na 2026.”

“Jagoranci ba wai cin zaɓe ba ne, sai dai ceton rayuka. Dole ne mu fifita tsaro da mutuncin ’yan Najeriya, mu ɗauki ran ɗan Adam a matsayin abu mafi muhimmanci.”

Obi ya kuma ce tarihi zai tuna da shugabanni ne bisa yadda suka ɗauki mataki wajen kare jama’a a irin wannan lokaci, ba wai dabarun siyasa ba.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *