‘Shekaru 40 ina sana’ar Ɗanwake’

[ad_1]



Malama Saudatu Ɗanjuma wacce aka fi sani da Yarinye Mai Ɗanwake, ta shafe shekara 40 tana sana’ar ɗan wake a unguwar Hawan Dawaki da ke Ƙaramar Hukumar Kumbotso a cikin Birnin Kano.

A yayin tattaunawarta da Aminiya ta bayyana cewa, tsawon shekarun da ta kwashe tana wannan sana’a ta samu alheri da ba za ta taɓa mantawa da shi ba.

“Na fara wannan sana’ar da ɗan ƙaramin kwano, a hankali kuma kasuwar ta ci gaba da bunƙasa, har yanzu kimanin kusan shekara 40.”

Ta ƙara da cewa, ta gwada yin wasu sana’o’in, amma dai babu wacce ta shiga ranta kuma har yanzu take kai kamar sana’ar ɗanwaken.

Ta ce, ‘‘A baya ba na wuce kwano uku, amma yanzu a kullum ina yin kwano shida tsakanin safe da dare, kuma Alhamdulillahi kullum yana ƙarewa’’.

Ta bayyana cewa, duk da ƙalubale da ta fuskanta a tafiyar, wannan bai sa ta yi ƙasa a guiwa ba, ta tsaya tsayin daka wajen ganin cewar ta ci gaba da wannan sana’a da ke rufa mata asiri.

“Jarina ya taɓa karyewa, saboda yau da gobe, amma ba a sani ba, na ɗauki fanteka na bayar, aka siyar min ita, inda kuma jarin ya sake dawowa,” in ji Yarinye Mai Ɗan Wake.

Ta ƙara da cewa “komai ruwa ko iska ba ma fashi, duk da muna gajiya, amma a hakan muke cijewa ni da ’ya’yana da jikata guda a yanzu.”

Ta shaida wa Aminya cewa, tabbas wannan tafiya tsawon shekara 40 tafiya ce mai cike da ƙalubale iri-iri, amma duk da yawan kira da aka yi a baya kan ta haƙura da wannan sana’a wannan bai sa ta yi ƙasa a guiwa ba.

Ta ce, a baya sana’ar ɗan wake kawai take yi, amma a yanzu ta ƙara da shinkafa da wake, amma dai har yanzu ɗan waken da shi ta fi shahara kuma da haka ake kiran gidanta.

A cikin wannan sana’a ta ɗan wake ta samu alheri mara misaltuwa, baya ga kadarori da dabbobi da ta saya, ta hanyar wannan sana’a, ta aurar da ’ya’yanta mata har biyu banda ’ya’yan ’yan uwa da kuma dangi da aka tallafa wa ta ko’ina.

Bugu da ƙari ta ce, a yanzu wannan sana’a ta zame masu tamkar jini da tsoka, domin kuwa har a yanzu ba ta fara tunanin dakatawa ba, kuma tana fatan ’ya’ya da jikokin su gaje ta a wannan sana’ar.

Har ila yau, Saude ta tabbatar da cewa, duk da tarin ayyukan da ke cikin wannan sana’a hakan bai sa ta hana ’ya’yanta da ke taimaka mata zuwa makaranta ba. Dukkaninsu suna zuwa makaranta ta addini da kuma boko. A yanzu mutum ɗaya ne daga cikinsu bai kammala

makarantar sakandare ba, kuma ba da jimawa ba ɗaya daga ’ya’yan nata ya yi saukar Alƙur’ani a Islamiyyarsu.

Mijin Saude Mai Ɗanwake, Alhaji Ayuba Yahaya Mai Katifar Rimi shi ma ya yi ƙarin haske a kan yadda ya ƙarfafa wa mai ɗakin nasa tun a baya lokacin da yake cikin wadata.

Shi ma ya bayyana mana cewa, shahararren ɗan kasuwa ne wanda ya ƙware wajen sarrafa audugar rimi wajen yin katifu da matasan kai.

Ya bayyana cewa, shi ya fara ba su jari ita da abokiyar zamanta, inda ita ya ba ta jarin ɗan wake, abokiyar zamanta kuma ya ba ta jarin koko.

Ya ce abokiyar zaman a halin yanzu ta daina, amma ita har yanzu tana yi, wanda yana yin alfahari da hakan.

“Ina jin daɗi idan na ga cewa, mutane za su zo, su sayi ɗan wake a gidana, domin kuwa wani zai zo ma ba shi da kuɗi, amma zan zo da kaina na karɓa na bayar, wanda wannan abin farin ciki ne a gare ni.”

Ya ƙara da cewa, ladan da Allah zai ba su a wannan sana’a duk da cewa saya ake shi ne babban abin da ke faranta masa rai duk lokacin da ya ga ana hadahadar ɗan wake a gidan.

Habiba Ayuba, wacce ita ma ’ya ce ga Saude Mai Ɗan wake ta ce, suna alfahari da wannan sana’a ta mahaifiyarsu, kuma suna fatan ta ci gaba da bunƙasa a koyaushe.

Ko da Aminiya ta zanta da masu sayen wannan ɗan wake, sun bayyana cewa, shekara aruaru suna jin daɗin ɗan waken, kuma, babban abin da ke burge su shi ne ba dare ba rana duk lokacin da mutum ya zo zai samu akwai ɗan wake a gidan.

Har ila yau, wani daga cikin masu sayen mai suna Ayuba Sulaiman ya ƙara da cewa, shi a yanzu a duk yankin Hawan Dawaki bai ga wani gida da ake arahar abinci ba a kamar gidan Yarinye wanda hakan ba ƙaramin faranta masa rai yake yi ba.

Ya ce da Naira 300 a yanzu mutum zai ci, ya ƙoshi. Ɗan waken 200 idan aka haɗa wa mutum da waken Naira 100 ya ishe shi tun safe har dare.

Mu’azu Yahaya, ya ce gidan ɗan wake ya zame masu tamkar gida, domin ko babu kuɗi zai ci ɗan wake, ya ƙoshi, kuma ko da ya zo da kuɗinsa, idan ya ce a ba shi na 100 to tabbas na 200 za a zuba masa, haka idan ya ce na 200 to ya san tabbas sai an ba shi na 300.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *